
Majalisar Wakilai ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na karɓo rancen dala miliyan 516.3 domin tallafa wa aikin gina wasu sassan babbar hanyar Sokoto zuwa Badagry.
An rawaito cewa majalisar ta bayar da amincewar ne a zamanta na ranar Talata bayan karanta wasikar shugaban kasa da kuma gabatar da rahoton kwamitin basussuka da lamuni, inda ta bukaci a rika gabatar da rahoton yadda ake kashe kudaden aikin duk bayan watanni uku.
Gwamnatin tarayya ta ce za a samo rancen ne ta hannun Deutsche Bank, domin aikin wasu sassa na hanyar mai tsawon kusan kilomita 120, yayin da za ta bayar da nata gudunmuwar kudin diyya da mallakar filaye.
Sai dai masu suka na nuna damuwa kan karin bashin kasashen waje, suna cewa ya kamata a tabbatar da gaskiya, inganci da kuma anfani kai tsaye ga al’umma kafin daukar karin rance.
A cewar gwamnati, aikin titin zai rage wahalar sufuri, bunkasa kasuwanci, hada yankunan Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma, tare da karfafa tattalin arzikin kasa idan an kammala shi.
