
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Olanipekun Olukoyede, ya bayyana cewa kusan ɗalibai shida cikin goma a jami’o’in Njjeriya na shiga harkar damfara ta intanet da aka sani da Yahoo Yahoo.
Ya ce, binciken hukumar ya nuna ƙaruwar laifukan damfarar, wato cybercrime a tsakanin ɗalibai, inda yawancin waɗanda ake kamawa ɗaliban ne.
Olukoyede ya kuma ambaci wani samame a Lagos da aka kama mutane 792, da dama daga cikinsu ɗalibai ne, abin da ke nuna girman matsalar.
Ya ƙara da cewa, binciken da hukumar ta yi cikin shekara guda ya nuna cewa dalibai da dama na shiga harkokin damfara ta yanar gizo, kuma da yawa daga cikin wadanda aka kama a ayyukan samame dalibai ne.
Haka kuma, yanzu an samun wani sabon salo na damfara da ake kira “Yahoo Plus”, inda wasu ke hada damfarar intanet da wasu al’adun tsafi.
A ƙarshe, ya buƙaci jami’o’i su fara amfani da fasahar Artificial Intelligence AI domin gano damfara da inganta gaskiya a harkokin ilimi.
