Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) sun yi watsi da duk wani ƙawancen siyasa ko tsarin da suke ganin zai iya yin barazana ga damar jam’iyyar da ’yan takararta a zaɓen 2027.
Gwamnonin sun ce ba za su shiga, goyi bayan ko amincewa da duk wani tsarin siyasa da zai iya raunana APC, yin illa ga ’yan takarar jam’iyyar ko kuma kawo cikas ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.
Shugaban ƙungiyar Gwamnonin APC, kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ne ya bayyana matsayar gwamnonin yayin da yake magana da manema labarai bayan kammala taron ƙungiyar a Abuja a daren Litinin.
Matsayar gwamnonin ta zo ne a daidai lokacin da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ke jagorantar wani tsarin da ake kira ‘Rainbow Coalition’, wanda ya ce an ƙirƙire shi ne domin tallafa wa sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.
Wannan yunƙuri ya fara ne a Jihar Ribas, inda Wike ya taɓa zama gwamna, kafin daga bisani ya yaɗu zuwa wasu sassan ƙasar.
Wasu jiga-jigan APC sun nuna damuwa kan kawancen, musamman bisa zargin cewa Wike na amfani da shi wajen tallafa wa ’yan siyasar da suka sha kaye a zaɓen fidda gwani na APC, waɗanda yanzu suke neman wasu kujerun zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).
Wike, wanda ke cikin manyan ’yan PDP kuma yake riƙe da mukami a gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin APC, ya zargi Uzodimma da Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ, da yaɗa labaran ƙarya game da kawancen.
A wata tattaunawa da manema labarai kwanan nan, ministan ya ce Uzodimma da AbdulRazaƙ ne ke da alhakin yaɗa waɗannan zarge-zarge saboda karuwar goyon baya da mambobin kawancen ke samu.
Wike ya kuma bayyana cewa duk da cewa kawancen na goyon bayan sake zaɓen Tinubu ne, yana kuma bai wa ’yan siyasar da ke son kalubalantar ’yan takarar APC a zaɓen gwamna da na Sanata na 2027 dama.
Uzodimma ya ce gwamnonin APC ba za su goyi bayan ko amincewa da wani ɗan takara da ba ɗan jam’iyyar APC ba a zaɓen 2027.
Ya ce: “ƙungiyar Gwamnonin APC baki ɗaya ta amince cewa mambobinta ba za su shiga, goyi bayan ko amincewa da duk wani kawance ko tsarin siyasa da zai iya yin illa ga sake zaɓen Shugaban ƙasa, raunana APC ko kuma yin illa ga wani ɗan takarar jam’iyyar a kowane mataki ba.”
Ya ƙara da cewa: “A taƙaice, ƙungiyar ba ta da niyyar goyon bayan wani ɗan takara a kowane mataki wanda ba ɗan takarar APC ba ne, domin jam’iyyarmu ce ke ɗaukar nauyin ’yan takarar da ke neman kujeru.”
Gwamnan ya ce yakin neman zaɓen APC a dukkan matakai zai mayar da hankali ne kan ’yan takarar jam’iyyar, tare da tafiya daidai da ajandar Shugaba Tinubu da manufofin jam’iyyar.
“Alƙawarin gwamnonin APC na yaƙin neman zaɓe ya kebanta ne ga dukkan ’yan takarar APC. Dukkan tsarin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a kowane mataki zai kasance bisa abin da Shugaban ƙasa yake bukata da kuma manufofin dabarun jam’iyyar,” in ji Uzodimma.
A nasa martanin, Wike ya ce Rainbow Coalition ba ta da alaƙa da APC, yana mai cewa ƙungiyar wani dandali ne na jam’iyyu daban-daban da ke tallafa wa sake zaɓen Tinubu.
Ya kuma bayyana cewa bai taɓa yin alkawarin cewa PDP ba za ta tsayar da ’yan takara a zaɓen gwamna, Majalisar Dokoki ta ƙasa da Majalisun Dokokin Jihohi ba.
