2027: INEC ta bai wa APC, PDP, ADC, NDC da sauran jam’iyyu damar ɗora ‘yan takararsu a shafinta

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bai wa jam’iyyun siyasa tara lambobin shiga (access codes) domin su fara loda sunayen ‘yan takararsu a shafin hukumar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Binciken jaridar Leadership ya nuna cewa jam’iyyun da suka samu lambobin sun haɗa da All Progressiɓes Congress (APC), Peoples Democratic Party (PDP), African Democratic Congress (ADC), Nigeria Democratic Congress (NDC) da wasu jam’iyyu masu rijista.

Ana sa ran jam’iyyun za su yi amfani da lambobin wajen loda sunayen ‘yan takararsu na kujerun Shugaban ƙasa, Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da kuma gwamna a jihohin ƙasar. Sai dai jihohin Kogi da Osun, waɗanda ke gudanar da zaɓen gwamna a lokuta dabam, ba sa cikin wannan tsari.

Wani babban jami’in INEC, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa Leadership cewa jam’iyyar NDC na cikin waɗanda aka bai wa lambobin shiga, yana mai musanta rahotannin da ke cewa an hana jam’iyyar damar shiga tsarin.

A cewarsa, babu gaskiya a ikirarin cewa INEC ta hana NDC lambar shiga domin loda sunayen ‘yan takararta.

“Hukumar ba ta da wani dalilin hana kowace jam’iyyar siyasa da aka yi wa rajista damar amfani da dandalin loda sunayen ‘yan takara. Zan iya tabbatar muku cewa NDC na cikin jam’iyyun da suka karɓi lambobin shiga,” in ji jami’in.

Wannan bayani ya zo ne bayan wasu jami’an jam’iyyar NDC sun yi zargin cewa ba su samu lambar shiga daga INEC ba, a daidai lokacin da jam’iyyar ke fuskantar ƙalubalen shari’a kan batun yi mata soke rajista.

A cewar wani jami’in jam’iyyar, Osa Director, sun je ofishin INEC domin karɓar lambar shiga, amma aka sanar da su cewa za a sake tuntubarsu daga baya.

“Mun je INEC domin karɓar lambar shiga da za mu yi amfani da ita wajen loda sunayen ‘yan takararmu, amma aka ce za a dawo mana da amsa. Saboda haka, bai kamata a ɗora wa jam’iyyar laifin jinkirin loda sunayen ‘yan takara ba,” inji shi.

Sai dai majiyar INEC ta jaddada cewa hukumar ta yi wa dukkan jam’iyyun da suka cancanta adalci da daidaito, tana mai ƙara da cewa ana sa ran ƙarin jam’iyyu za su samu lambobin shiga kafin ƙarshen ranar Litinin.

Jami’in ya bayyana cewa adadin jam’iyyun da za su samu damar shiga tsarin na iya ƙaruwa zuwa 13 kafin ƙarshen ranar.

Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da jita-jitar da ke cewa wasu jam’iyyu za a hana su amfani da tsarin tantance ‘yan takara na INEC, yana mai jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da tabbatar da adalci da bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar shiga zaɓen 2027 ba tare da nuna bambanci ba.

By ukarofi

Leave a Reply