Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A wani gagarumin yunƙuri na bunƙasa rayuwar mata da inganta walwalar al’umma, Gidauniyar Sidiya Charity Foundation ta ƙaddamar da wani shiri na musamman na horas da mata sana’o’i da dabarun dogaro da kai, domin ba su damar samun hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma ƙarfafa matsayinsu a fannin tattalin arziki.
An ƙaddamar da shirin ne cikin yanayi na farin ciki da fatan alheri, inda manyan baƙi, shugabannin al’umma, masu ruwa da tsaki da sauran masu goyon bayan ayyukan ci gaba suka halarci taron domin nuna goyon bayansu ga wannan shiri.
Da take jawabi a wajen taron, Shugabar Gidauniyar Sidiya Charity Foundation, Hajiya Sadiya Sidi Said, ta bayyana cewa manufar shirin ita ce samar wa mata ilimi da ƙwarewar sana’o’i da za su taimaka musu wajen dogaro da kansu, rage zaman banza da kuma ba da gudunmawa ga ci gaban iyalansu da al’ummarsu.
Ta ce, ci gaban kowace al’umma yana da alaƙa kai tsaye da irin damar da ake bai wa mata, tana mai jaddada cewa mace mai ilimi da sana’a na taka muhimmiyar rawa wajen gina iyali mai ƙarfi da al’umma mai ci gaba.
“Lokacin da ka ba mace dama, ba mutum ɗaya ka canja ba; kana canza iyali, kana gina al’umma, kana kuma sauya makomar ƙasa,” inji Hajiya Sadiya.
A cewarta, shirin zai ƙunshi horaswa a fannoni daban-daban da suka haɗa da sana’o’in hannu, dabarun kasuwanci, hanyoyin tafiyar da ƙananan sana’o’i da kuma shawarwari kan yadda mahalarta za su bunƙasa harkokinsu cikin nasara.
Waɗanda suka halarci taron sun yaba da wannan shiri, suna masu cewa irin waɗannan matakai na taimakawa wajen rage talauci, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa mata su zama masu bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki.
Gidauniyar ta kuma yi kira ga gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu, kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane da su haɗa hannu wajen tallafa wa irin waɗannan shirye-shirye domin samar da al’umma mai ɗorewar ci gaba da wadatar arziki.
