Daga ABUBAKAR A BOLARI, Gombe
Dan takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, Sardaunan Gombe, ya bayyana ƙudirinsa na gina gwamnati da zai yi tafiya da kowa tare da bunƙasa ci gaba idan aka zaɓe shi a shekarar 2027.
Gwamna ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jam’iyya, masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar, inda ya ce babban burinsa shi ne haɗa kan jama’a da tabbatar da ci gaban da zai amfani kowa da kowa.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Sani Shawai, ya fitar, Gwamna ya ce manufarsa ta “Gombe First” za ta mayar da hankali ne wajen fifita muradun jama’ar jihar fiye da anfani na siyasa ko na ƙashin kai.
“Burina shi ne ganin Gombe ta zama jihar da kowa zai ji yana da muhimmanci, kuma gwamnati za ta yi aiki domin ci gaban al’umma baki ɗaya,” in ji shi.
Ya tabbatar da cewa idan ya zama gwamna, gwamnatinsa za ta kasance mai adalci da kofa a bude ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.
Dan takarar ya kuma yi alƙawarin bai wa mata, matasa da marasa ƙarfi damar shiga harkokin gwamnati da yanke shawara.
Haka kuma, ya yi kira ga sauran masu neman takara a APC da su haɗa kai domin cimma burin gina Gombe mai cike da zaman lafiya da ci gaba.
“Dukkanmu muna son ci gaban Gombe. Idan muka haɗa kai, za mu iya gina jihar da za ta zama abin alfahari,” in ji shi.
Gwamna ya yabawa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa ayyukan ci gaba da aka gudanar a ɓangarorin ilimi, lafiya, hanyoyi da tattalin arziki, yana mai cewa zai ci gaba daga inda aka tsaya.
Ya bayyana noma, ilimi, kiwon lafiya, bunƙasa matasa, samar da ababen more rayuwa da ci gaban rayuwar jama’a a matsayin manyan abubuwan da zai bai wa fifiko.
Har ila yau, ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya ƙarƙashin ajandar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin jawo ƙarin ayyukan ci gaba da samar da tattalin arziki zuwa jihar.
Lokaci ya yi da za mu fifita haɗin kai da ci gaba sama da rikicin siyasa,” in ji shi
A ƙarshe, ya buƙaci al’ummar Gombe da su rungumi haɗin kai tare da marawa shugabanci nagari baya kafin zaɓen 2027.
