Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gabanin babban zaɓe na 2027, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana goyon bayansa ga Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP).
Mohammed, wanda ya karɓi baƙuncin ɗan takarar Shugaban ƙasa a 2023 na LP a gidan Gwamnatin Jihar Bauchi jiya Alhamis ya ce, a shirye yake ya yi aiki da Obi.
Ganawar ta sirri, ta kwashe sama da awa ɗaya ana gudanar da ita a Gidan Ramat da ke Bauchi bayan ganawa da manema labarai.
Sai dai babu wata jam’iyya da ta yi ƙarin haske kan ko taron zai haifar da ƙawancen siyasa ko akasin haka.
“A matsayina na mutum, a shirye na ke na yi aiki da Peter Obi don ganin mun haɗu, mun haɗa kai, tare da samar da kyakkyawan shugabanci a ƙasar nan. Za mu samar da ƙwaƙƙwaran adawa tare da ilimi, lokaci, da hangen nesa ta hanyar da za ta taimaka wajen ceto da kuma dawo da ƙasarmu daga masu neman durƙusar da ita,” inji Mohammed.
“Za mu ɗauke shi kuma mu ciyar da shi gaba ta yadda za a ci gaba, za ku ga ƙarin ayyukan haɗin gwiwa tsakanin mu, Obi, Gwamnonin PDP, da PDP a matsayin jam’iyya.”
