Daga UMAR GARBA a Katsina
Wasu mutane ɗauke da muggan makamai da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi awon gaba da Abdulsalam Rabi’u Faskari, matashi kuma zakaran musabaƙar karatun Al’ƙur’ani ta ƙasa tare da mahaifinsa, Malam Rabe Faskari, da wasu ‘yan uwansa lamarin ya faru a kusa da Labin Bangori a Jihar Katsina.
Harin ya faru ne a daidai lokacin da gwarzon musaƙar ke koma wa gida tare da mahaifinsa da sauran ‘yan uwansa bayan da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya karrama Abdulsalam da kyaututtuka bisa nasarar da ya samu inda ya zo a matsayi na ɗaya a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin-Kebbi, Babban Birnin jihar Kebbi.
Wani jami’in gwamnati a ƙaramar Hukumar Faskari da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce, “an sace Malam Rabe da ‘ya’yansa biyar, ciki har da Abdulsalam a Bangori da ke kan titin ‘Yankara. Tun daga nan ba mu ji ɗuriyarsu ba.”
Baya ga kasancewar Abdulsalam hafizin A’lƙur’ani, ɗalibi ne kuma dake karatun koyon aikin likitanci a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, ya samu matsayi na ɗaya a ɓangaren maza na haddar Hizb 60 na Alƙur’ani mai girma.
ƙungiyar ɗalibai Musulmi ta Nijeriya (MSSN) ta yi Allawadai da sace fitaccen ɗalibin wanda shine limamin masallacin Kwalejin Kimiyyar aikin likita a Jami’ar ta A.B.U.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta aike wa manema labarai ciki har da jaridar Blueprint Manhaja ta ce, “Cikin tsananin damuwa da baƙin ciki, ƙungiyar ɗalibai musulmi ta Najeriya (MSSN) ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta bayyana matuƙar baƙin cikinta gami da jajantawa ga ‘yan uwa da abokan arziƙi da abokan karatunsa da ɗaukacin al’ummar Musulmi bisa garkuwa da aka yi da ɗan uwanmu masoyinmu, Abdussalam Rabi’u Faskari.
Kawo yanzu kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiƙ Aliyu, bai yi ƙarin haske ba game da lamarin.
