2027: Nasarar Tinubu za ta kawo ƙarshen siyasar wasu shugabannin adawa – Amaechi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), kuma tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya faɗa wa shugabannin jam’iyyar cewa nasarar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu a zaɓen 2027 za ta iya sa da dama daga cikinsu su daina siyasa.

Amaechi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron ƙungiyar mata ta ƙasa ta ADC, wato ADC National Women League Conference, da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.

Ya yi nuni da yadda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kayar da Peoples Democratic Party (PDP) a matakin tarayya a zaɓen 2015, inda ya buƙaci matan ADC da su koma jihohinsu da mazabunsu domin gudanar da gangamin neman ƙuri’u, yana mai cewa hakan ne kaɗai zai ba ADC damar ƙalubalantar APC a zaɓen 2027.

Amaechi ya ce, “Idan ba ka fito daga FCT ba, koma gida ka yi yaƙin neman zaɓe. Ni zan tafi ranar Laraba, ba zan sa kwat ba, zan sanya kaya irin na matashi. Bari in gaya muku abin da zai faru. Mu shugabannin da kuke gani a nan, idan APC ta lashe zaɓen 2027, za a yi ritaya da mu daga siyasa. Don haka, idan ba ku son a yi mana ritaya daga siyasa, dole mu koma gida.”

Ya kuma buƙaci matan da su taimaka wajen samar da ƙuri’u a matakin unguwanni, yana cewa idan aka samu ƙuri’u 2,000 daga kowace mazaba, hakan zai taimaka wajen samun nasarar zaɓen. Ya ce zai gudanar da yaƙin neman zaɓe a wurare daban-daban, ciki har da Kebbi, Yola, Rivers da Delta, musamman a zaɓukan gwamnonin jihohi, saboda ɗan takarar shugaban ƙasa ba zai iya gudanar da mulki yadda ya kamata ba tare da samun gwamnoni ba.

Tsohon Ministan Sufuri ya ce APC ta yi amfani da mata wajen kayar da PDP a zaɓen 2015.

Ya ce, “Lokacin da muke APC kuma muna son cire gwamnatin ku, kun ga abin da muka yi. Mun fito da mata. A duk jihar da muka je, mata ne suke gaba. Mun yi magana da su, mun gana da su da dare, kuma mun tabbatar mun gaya musu cewa idan ba su fito sun yi zaɓe ba, ba za mu yi nasara ba. Sai suka fito. Mun yi yaƙin, kuma muka yi nasara.”

Amaechi ya kuma danganta kiran da yake yi na ƙara kaimi wajen neman ƙuri’u da matsalolin tattalin arziki da ya ce ’yan Nijeriya ke fuskanta a yanzu. Ya tambayi mahalarta taron ko suna iya biyan kuɗin makaranta ko sayen abinci cikin sauƙi, yana kwatanta halin da ake ciki yanzu da lokacin da ya ce yana cikin gwamnatin APC.

Ya ce, “A wancan lokacin, Nijeriya ba ta cikin tsananin yunwa kamar yanzu. Nijeriya tana iya samun wasu abinci, ko ba haka ba? Yanzu, nawa ne daga cikinku za su iya samun kuɗin abinci? Nawa ne za su iya biyan kuɗin makaranta ba tare da aika saƙo ga Dino (Sanata Dino Melaye) ko wani mutum ya ba su kuɗin makaranta ba?”

Ya kuma yi ikirarin cewa adadin ’yan Nijeriya da ke shiga cikin talauci yana ƙaruwa, tare da cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya ƙaru daga tsakanin miliyan 10 zuwa 12 a lokacin da ya bar gwamnati zuwa kusan miliyan 20 a yanzu. Ya ce wannan yana nuna yadda ake ƙara jefa ’yan Nijeriya cikin talauci, musamman a yankin Arewa. Waɗannan alkaluman dai zarge-zargen Amaechi ne a cikin jawabin nasa.

Amaechi ya ce, “Kowane mako, ’yan Nijeriya 10 suna shiga cikin talauci. Idan aka gaya muku adadin ’yan Nijeriya da suka mutu, za ku yi mamaki. Lokacin da na bar gwamnati a APC, ina ba ku alkaluma yanzu, akwai yara miliyan 10 zuwa 12 da ba sa zuwa makaranta. Yanzu akwai miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta.”

Ya ƙara da cewa, “Idan kai ɗan Arewa ne kuma kana zaune a nan, bai kamata ma ka rika waƙa ba. Dalili kuwa shi ne Tinubu yana ƙara jefa ka cikin talauci a kowace rana. Abin da ya kamata ka yi shi ne ka ɗauki wannan yaƙi a hannunka. Idan dukkan matan Arewa suka fito suka yi zaɓe, Tinubu ba zai iya bayyana wani sakamako ba.”

A nata jawabin, Hajiya Titi Atiku Abubakar ta ce lokaci ya yi da ’yan Nijeriya za su mayar da hankali wajen kyautata rayuwar ƙasar, inda ta buƙaci matan da kada su bari a tsoratar da su.

Ta buƙace su da su koma cikin al’umma domin tattaunawa da abokansu, maƙwabtansu da sauran jama’a, tare da neman su goyi bayan ’yan takarar ADC a zaɓen 2027.

Titi Atiku ta ce, “Idan ka je kasuwa, ba za ka iya sayen komai ba, har da magani. Jiya na aika a saya min magani. Maganin da muka saba saya kan N400 yanzu ya koma N1,000. Na kasa yarda da abin da idona ya gani. To ina kuɗin suke? Kuma muna cikin tsarin rashin amfani da kuɗin hannu, wanda har kuɗaɗen ma ana cire su.”

Ta ƙara da cewa wasu ma’aikata da ’yan kwangila na aiki amma ba sa samun kuɗaɗensu, tana mai cewa hakan na faruwa ne saboda goyon bayan ADC. Ta ce ADC ba ta da isassun kuɗaɗe, amma dole ne su nemi abin da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu.

Titi Atiku ta kuma ce tsadar rayuwa na hana yara da dama zuwa makaranta, inda ta roƙi matan da kada su bari ’yan siyasa su rinjaye su da abinci ko wasu abubuwa a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ta ce, “Yawancin yaranmu ba sa zuwa makaranta saboda tsadar rayuwa ta yi yawa. Don haka, mata, ina roƙonku. Mata, ina roƙonku, kada ku bari su zo su saye ku da abinci. Dole mu je kowane lungu da saƙo na Nijeriya, musamman wuraren da mutanen ƙauyuka suke.”

Jawaban na Amaechi da Titi Atiku sun zo ne yayin da ayyukan siyasa da gangamin jam’iyyu ke ƙara ƙamari gabanin zaɓen 2027, inda ADC ke ƙara ƙarfafa shirye-shiryenta na neman ƙuri’u a matakin jihohi da ƙananan hukumomi da mazabu.

By ukarofi

Leave a Reply