Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta bayyana shirin gudanar da cikakken bincike kan bashin da jihar ke bi, kwangilolin ayyuka da yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati, a matsayin wani ɓangare na manufofinta na kamfen ɗin zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce za ta mayar da hankali kan yadda gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ke gudanar da harkokin kuɗaɗe da ayyukan raya ƙasa, musamman a fannonin ilimi, lafiya, noma da samar da ababen more rayuwa.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na kwamitin yaƙin neman zaɓen PDP a jihar, Ahmed Shuaibu Gara, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce jam’iyyar za ta gudanar da kamfen bisa muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar al’ummar jihar.
Gara ya bayyana cewa binciken da PDP ke shirin yi zai shafi bashin da ake bin jihar, rance-rancen da gwamnati ta karɓa, yadda ake kashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi, hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga, harkokin filaye, ɗaukar ma’aikata da ƙarin girma a ma’aikatan gwamnati.
Ya ce jam’iyyar za ta kuma binciki yadda ake aiwatar da ayyuka da shirye-shirye a hukumomi da ma’aikatun gwamnati, ciki har da GOGIS, GOSUPDA, Hukumar Tara Haraji ta Jiha, Go-Health, BESDA, ACReSAL da RUWASA.
A cewarsa, binciken zai ƙunshi kwangilolin gina hanyoyi, samar da ruwan sha, yaƙi da zaizayar ƙasa, bunƙasa makamashi, shirye-shiryen kiwo, rabon takin zamani da kayan tallafin noma, da kuma sayen kayan aikin asibitoci.
Haka kuma, PDP za ta duba ayyukan Gombe Line, Ashaka da Kolmani, tallafin karatu, alawus-alawus na malamai da ma’aikatan lafiya, kuɗaɗen bunƙasa wasanni da kuma harkokin hukumomin sarakunan gargajiya.
Sauran abubuwan da jam’iyyar ta ce za ta bincika sun haɗa da kuɗaɗen yaɗa labaran gwamnati, ayyukan ofishin matar gwamna, kuɗaɗen aikin Hajji da ziyarar Kudus, sayen motocin jami’an siyasa da kuma tallafin ayyukan haɗin gwiwa.
Gara ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta nazarci rahotannin kwamitocin da aka kafa domin duba manyan makarantun jihar, da kuma tallafin da gwamnati ta bayar ga mutanen da bala’o’i da rikice-rikicen al’umma suka shafa.
Ya jaddada cewa PDP za ta gudanar da kamfen cikin mutunci da balaga, ta hanyar tattauna manufofi, ayyuka da nasarorin da aka samu, maimakon kai hare-haren kashin kai ga abokan hamayyar siyasa.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa jam’iyyar ba za ta yi shiru ba idan aka samu amfani da zagi, tsoratarwa, tashin hankali ko lalata kadarori a yayin harkokin siyasa.
Ya ce PDP na da burin dawo da amincewar al’umma ga shugabanci, tare da tabbatar da cewa ‘yan takararta za su kasance masu riƙon amana, gaskiya da sauraron buƙatun mutanen da suke wakilta.
Gara ya bayyana cewa jam’iyyar na kuma shirin ƙulla yarjejeniyar zamantakewa da al’ummar Gombe domin tabbatar da cewa manufofi da ayyukan gwamnati za su kasance bisa buƙatu da muradun jama’a.
