2027: Sanata Marafa ya ƙaddamar da kwamitin mutum 53 don yin takarar gwamna a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sanata Kabiru Garba Marafa ya ƙaddamar da kwamitin mutum 53 mai taken ƙungiyar Marafa don takarar Gwamna a 2027, (Marafa Muka) a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryensa na tsayawa takarar gwamna a 2027 a jihar Zamfara.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan ƙaddamar da kwamitin da aka gudanar a hedikwatar kamfen ɗinsa da ke Gusau a yau Laraba, Sanata Marafa ya buƙace su da su kasance masu kishin ƙasa wajen sauke babban nauyin da ke kansu.

A cewarsa, ayyukan da ke gaban kwamitin shine samar da dimbin magoya bayan sa don kai wa ga nasarar da aka sanya a gaba.

Ko da yake, Sanata Kabiru Garba Marafa bai ambaci jam’iyyar siyasa da zai tsaya takara ba, yana mai cewa lokaci ya yi da za a ceto mutanen Zamfara daga rashin tsaro da ke addabar jihar.

Sanata Marafa wanda na hannun damar sa a siyasa, Alh. Usman S Fada ya wakilce shi a wurin bikin rantsar da kwamitin, ya sake jaddada cewa zai tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rasa ƙuri’u sama da miliyan ɗaya a jihar Zamfara a shekarar 2027.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa waɗanda aka rantsar cikin kwamitin mutum 53, sun haɗa da Dr. Abubakar Usman Gora a matsayin shugaba, Hon. Bello B S Kaura a matsayin mataimakin shugaba da kuma Auwal Garba Alhazzai a matsayin sakatare da sauransu.

Idan za a iya tunawa, Sanata Kabiru Garba Marafa ya fice daga jam’iyyarsa ta APC a jihar Zamfara a kwanakin baya.

A cikin wani saƙon fatan alheri, shugaban ƙungiyar tafiyar siyasar Sanata Kabiru Garba Marafa, Alh. Surajo Maikatako, ya tabbatar wa mambobin kwamitin cewa za su haɗa kai domin cimma nasarar burin Sanata Kabiru Garba Marafa a shekarar 2027 a jihar.

By ukarofi