
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Farouk Ahmed ya sauka a muƙamin shugabancin Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA) yayin da Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yi zargin rashawa akansa.
Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da haka a wata takarda a yau Laraba, inda ya kuma ce Gbenga Komolafe ya bar muƙaminsa na Shugaban Hukumar Gudanarwar Harkokin Man Fetur ta ƙasa, wato NUPRC.
Onanuga ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen mutum biyu domin maye guraben da suka bari.
Shugaban Ƙasar ya bada sunan Oritsemeyiwa Eyesan a matsayin shugaban (CEO) NUPRC da kuma Sa’idu Mohammed a shugabancin NMDPRA.
