Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Da wannan mataki da gwamna Raɗɗa ya ɗauka na mika dajin kogo da ke ƙaramar hukumar Faskari ga Gwamnatin tarayya zai ƙarfafa kare muhalli da inganta ɗorewar kula da gandun daji.
Gwamnan ya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU) a fadar gwamnatin Katsina bayan kammala taron kwanaki biyu na majalisar ƙasa kan muhalli karo na 18, da kuma ziyarar girmamawa daga ministan muhalli, Mallam Balarabe Abbas Lawal.
“Mun miƙa dajin kogo a hukumance ga Gwamnatin Tarayya bisa ga manufarmu ta bai ɗaya wajen tabbatar da ɗorewar muhalli,” in ji Gwamna Raɗɗa.
Gwamnan ya yi amfani da damar wajen nuna cigaban da Katsina ke samu, inda ya ce karɓar baƙuncin majalisar ya ba mahalarta damar ganin cigaban jihar da idonsu.
“Wannan taro ya bai wa baƙinmu damar ganin Katsina da kansu, su fahimci juriyar jama’armu da karamcinmu, tare da ganin irin cigaban da muke samu fiye da mummunan hoton da ake yawan nunawa a kafafen yaɗa labarai,” in ji shi.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa Jihar Katsina na aiwatar da shirin samar da makamashi mai sabuntawa cikin gaggawa, da nufin samar da megawatt 25 na wutar lantarki ta hasken rana zuwa shekarar mai zuwa, tare da ƙarin megawatt 10 da ke kan hanya.
“Mun miƙa wani aikin injin iska (windmill), kuma ana ci gaba da matakan tarayya domin fara aiki gaba ɗaya. Haka kuma, Jihar Katsina na aiwatar da aikin wutar lantarki na haɗin iska da rana na farko a Nijeriya a Lambar Rimi, wanda aka tsara zai samar da megawatt 12 a cikin yankin tattalin arzikin kore (Green Economy Zone) namu,” Dikko ya ce.
Gwamnan ya bayyana cewa jihar ta gano manyan cibiyoyin gwamnati 12 da ke cin kusan kashi 92 cikin 100 na wutar lantarkin gwamnati, kuma an fara mayar da su zuwa amfani da makamashi mai sabuntawa.
“Fadar gwamnati yanzu tana aiki da tsarin solar mai megawatt ɗaya, an haɗa babban asibiti, kuma sakateriyar jiha gaba ɗaya tana amfani da wutar solar ba tare da dogaro da layin wutar ƙasa ba,” in ji Raɗɗa.
Dangane da tsaron muhalli, gwamnan ya nuna sare dazuzzuka a matsayin babbar barazana a yankin da ƙasa baki ɗaya, yana mai gargaɗi cewa kasuwancin gawayi na kasuwanci na ƙara alaƙantuwa da ƙungiyoyin laifi masu tsari.
“Tsakanin kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na dazuzzukanmu ba su ƙarƙashin kulawa, lamarin da ke haifar da babbar barazana ga muhalli da tsaron ƙasa, wanda ke buƙatar ɗaukar mataki mai ƙarfi daga Gwamnatin Tarayya,” ya gargaɗa.
Gwamna Raɗɗa ya yaba musamman da tasirin shirin ACReSAL a ƙananan hukumomin Jibia da Kaita, inda ya ce tsoma bakin shirin ya hana aukuwar ambaliyar ruwa a jihar a bara.
Ya ƙara da cewa Jihar Katsina ta samu amincewa don aiwatar da aikin wutar lantarki ta ruwa (hydroelectric) mai megawatt ɗaya a dam ɗin Danja, tare da haɗin gwiwa da ma’aikatar baitul-malin Faransa, kuma za a maimaita irin wannan aiki a sauran dam-dam na jihar.
Tun da farko, Ministan Muhalli, Mallam Balarabe Abbas Lawal, ya bayyana cewa Jihar Katsina ta inganta matsayinta a ƙimar ayyukan muhalli na ƙasa daga matsayi na uku zuwa matsayi na biyu.
“Katsina yanzu tana iya gogayya da jihohi da ke da albarkatu masu yawa fiye da ita,” in ji shi.
