
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jigo a jam’iyyar APC, Alwan Hassan ya ce kaso 95 na ministocin da suka yi aiki a zamanin mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dace a kama su, yana mai zargin an tafka rashawa da rashin binciken ayyuka, lamarin da ya sa yake ganin akwai buƙatar a gurfanar da su a gaban shari’a.
Alwan Hassan ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television, wanda Seun Okinbaloye ke gabatarwa.
Ya ce, gwamnatin Buhari ta gaza sanya ingantaccen sa ido, tare da bai wa ministoci cikakken ƴanci akan kuɗaɗen gwamnati.
Ya bayyana cewa, idan aka yi cikakken bincike kan bayanan gwamnati, kashi 95 cikin 100 na ministocin da suka yi aiki a tsawon shekaru takwas na mulkin Buhari ya kamata su kasance a gidan yari.
“Ba a taɓa samun lokacin da aka bai wa ministoci cikakken ƴanci ba tare da wani tsari na sa ido ba kamar a zamanin Buhari”, inji shi.
A cewarsa, an saki kasafin kuɗinsu na ayyuka gaba ɗaya, kuma babu wanda ya tambayi yadda aka kashe kuɗin.
“Idan aka buɗe littattafan kuɗi, kashi 95 cikin 100 daga cikinsu ya kamata su kasance a gidan yari zuwa yanzu. Kimanin kashi biyar cikin 100 ne kawai suka yi aiki nagari”, kamar yadda ya bayyana.
