2027: Sanata Onawo ya zama ɗan takarar gwamnan Nasarawa a APM

Spread the love

DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya

A yanzu haka Sanata Mohammed Ogoshi Onawo mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Kudu a majalisar dattawa na tarayya ne ya fito a matsayin ɗan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement wato APM a zaɓen 2027 mai zuwa.

An zaɓi Onawo ne a yayin babban taro na musamman na ‘yan wakilai na jam’iyyar wanda aka gudanar a yau Asabar a Lafia babban birnin jihar Inda aka tabbatar da shi ta hanyar amincewa baki ɗaya daga duka ‘yan wakilan da suka fito daga ƙananan hukumomi 13 na jihar.

Wakilin mu a jihar John D. Wada ya ruwaito cewa an gudanar da wannan taro ne domin cike gurbin da Dr. Mohamed Auwal ya bari wanda shi ne shugaban jam’iyyar APM na jihar Nasarawa ɗin kuma ɗan takarar da ya janye wa sanatan.

Bayan an tabbatar da shi a hukumance Onawo ya godewa ‘yan jam’iyyar bisa amincewar da suka ba shi. Ya kuma yi alƙawarin gudanar da kamfen mai maida hankali kan batutuwa da zai haɗa da kowa tare da mayar da hankali kan tsaro da raya ababen more rayuwa da noma da ilimi da samar da ayyukan yi da sauran su.

“Ina karɓar wannan naɗin da tawali’u da kuma kuduri mai karfi na yiwa al’ummar jihar Nasarawa hidima. Tare da APM zamu gina jihar da kowane ɗan ƙasa zai samu dama da bege,” in ji shi.

Sanatan ya kuma ce shi ne ɗan takarar da ya fi kowa ƙwarewa a yanzu saboda ya taɓa zama dan majalisar dokokin jihar sannan ya yi wa’adi biyu a majalisar wakilai ta ƙasa yanzu kuma yana majalisar dattawa.

Onawo ya bayyana cewa ya zo da ƙwarewar siyasa da kuma ƙwarewa a harkokin majalisa da kuma tsarin siyasa mai tushe a ƙasa musamman a Nasarawa ta Kudu, kuma shi ne madadin da ya dace ga mutanen jihar a 2027.

“A matsayina na ɗan majalisar wakilai na tsawon wa’adi biyu da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar nan kuma yanzu sanata, na gina kawance a faɗin jihar nan da waje. Saboda haka da yardar Allah zan zama gwamnan jihar nan tamu ta Nasarawa a zaɓe mai zuwa,” in ji shi.

Yayi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta kasance ta al’umma kuma za ta mai da hankali kan samar da wadata ga kowane gida ta hanyar amfani da abin da ya samu a baya da kuma yanzu.

Onawo ya bayyana kyakkyawan fata cewa APM za ta lashe kujerar gwamnan jihar da sauran kujerun siyasan a duka matakai idan hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta gudanar da zaɓe mai inganci da adalci da kuma gaskiya a 2027.

A baya, Auwal a cikin jawabinsa ya ce ya janye wa Sanata Onawo ne domin cigaban haɗin kan jam’iyyar da kuma tallafawa ɗan takarar da yafi kowa yaɗuwa kafin zaɓen 2027.

Shugaban jam’iyyar na jihar ya kuma bayyana Onawo a matsayin ɗan siyasa mai farin jini gun jama’a wanda ke da ƙwarewa da ƙarfin jagoranci sannan yace jam’iyyar ta shirya tsaf don yin aiki a dukkan ƙananan hukumomi 13 domin samun nasara.

Jami’an INEC da hukumomin tsaro ne suka sa ido kan yadda aka gudanar da taron.

By ukarofi

Leave a Reply