2027: Zulum ya goyi bayan tsohon kwamishina, Gubio don tsaya wa takarar gwamnan Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da goyon baya tsohon Kwamishinan Ayyuka, Mustapha Gubio don tsaya wa takarar gwamna a jihar, yayin babban zaɓen 2027.

Malam Dauda Iliya, wato Mai ba gwamnan shawara akan harkokin yada labarai ya tabbatar da haka ga NewsPointNigeria, jim-kaɗan bayan karɓar baƙuncin Gubio, wanda ya mallaki fom ɗin tsayawa takara a Abuja.

A wannan ci-gaba, an ga yadda hotunan da mai ba gwamnan shawara ya yaɗa suna nuna Mustapha Gubio na gabatar da fom ɗin nasa ga Gwamna Zulum.

Wannan goyon baya ta haifar da cece-kuce a fannin siyasar jihar musamman acikin ‘yan jam’iyyar APC, lamarin da ƙwararru ke ganin ka iya haddasa rarrabuwar kai acikinta.

Haka kuma, al’amarin ya nuna cewa akwai kamshin gaskiya a game da rikicin cikin gida da wasu mambobin jam’iyyar da suka jima suna hidimta mata.

By Babaji