Tinubu ya ba jakadun Nijeriya filaye a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya amince da wani muhimmin shiri na bai wa jakadu da manyan jami’an difulomasiyya filaye a birnin don ƙarfafa hulɗar ƙasa da ƙasa da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Wike ya bayyana cewa wannan mataki ba wai kawai don kyautata zamantakewar jakadun ba ne, har ma wata dabara ce ta ƙara kusantar Najeriya da ƙasashen waje ta fuskar diflomasiyya.

A cewarsa, idan jakadu sun samu kyakkyawan muhalli da damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi, hakan zai ƙara inganta hulɗa tsakanin Najeriya da ƙasashen da suke wakilta.

Ya ƙara da cewa gwamnati na sa ran wannan tsari zai buɗe ƙofofi ga sababbin jarin waje (FDI), musamman a fannoni masu matuƙar muhimmanci kamar noma, sarrafa shara, gine-gine da kuma sauran ayyukan raya birane. A cewarsa, Abuja na da damar zama cibiyar diflomasiyya mai ƙarfi a Afirka idan aka ci gaba da samar da irin waɗannan tsare-tsare.

Haka kuma, Wike ya yi kira ga jakadu da su zama jakadu na gaskiya wajen tallata Najeriya a ƙasashensu, ta hanyar nuna damar zuba jari da ƙasar ke da su.

Ya jaddada cewa Najeriya na da albarkatun ƙasa, ƙarfin matasa, da kuma kasuwa mai faɗi da za su iya jan hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya.

A ƙarshe, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, ta hanyar inganta tsaro, dokoki da kuma ababen more rayuwa, domin tabbatar da cewa duk wanda ya zo zuba jari a Nijeriya zai samu riba da kariya.

By Babaji