WHO: Nijeriya na cikin ƙasashen da suka fi samun yawan mutuwa daga ciwon hanta

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana Najeriya a cikin jerin ƙasashe goma da ke da mafi yawan mace-macen da ke da alaƙa da cutar hanta (hepatitis) a duniya, lamarin da ya sake janyo damuwa kan yadda cutar ke ƙaruwa da kuma jinkirin da ake samu wajen shawo kanta.

Rahoton cutar hanta na duniya na shekarar 2026 ya nuna cewa cututtukan hepatitis B da C, waɗanda ke haddasa kashi 95 cikin 100 na mace-macen da ke da alaƙa da cutar, sun yi sanadin mutuwar mutane kimanin miliyan 1.34 a shekarar 2024, yayin da sabbin masu kamuwa da cutar suka kai kusan miliyan 1.8 a duk shekara.

Rahoton ya ƙara da cewa ƙasashe goma da suka haɗa da Bangladesh, China, Ethiopia, Ghana, India, Indonesia, Najeriya, Philippines, Afirka ta Kudu da Vietnam sun kai kashi 69 cikin 100 na mace-macen hepatitis B a duniya. Haka kuma, Najeriya na cikin ƙasashen da ke da kashi 58 cikin 100 na mace-macen hepatitis C a duniya.

An kiyasta cewa mutane kimanin miliyan 287 na rayuwa da cutar hepatitis B ko C mai ɗorewa a shekarar 2024. A wannan shekarar, mutane miliyan 0.9 sun kamu da hepatitis B, inda yankin Afirka ya ɗauki kashi 68 cikin 100 na sabbin kamuwa, amma kashi 17 cikin 100 kacal na jarirai ne suka samu allurar rigakafin haihuwa.

Hukumar ta kuma bayyana cewa an samu sabbin kamuwa da hepatitis C kusan miliyan 0.9, inda masu amfani da allura wajen shan miyagun ƙwayoyi suka kai kashi 44 cikin 100 na sabbin kamuwa.

Duk da waɗannan ƙalubale, WHO ta ce ana fara samun ci gaba, inda sabbin kamuwa da hepatitis B suka ragu da kashi 32 tun daga shekarar 2015, yayin da mace-macen hepatitis C suka ragu da kashi 12 a duniya.

Daraktan Janar na WHO, Tedros Ghebreyesus, ya ce duk da cewa ana iya kawar da cutar, har yanzu ana tafiya a hankali, kuma mutane da dama ba a gano cutar a jikinsu ba ko kuma ba su samu magani ba.

WHO ta buƙaci gwamnatoci su ƙara ƙoƙari ta hanyar faɗaɗa allurar rigakafi, inganta gwaje-gwaje da magani, tabbatar da tsaron amfani da allura, da kuma haɗa ayyukan kula da cutar hanta cikin tsarin kiwon lafiya na farko.

By ukarofi