Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnonin jihohin Kwara, Sokoto da Yobe za su ƙaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar a jihar Katsina.
A wata hira da manema labarai a gidann gwamnatin Katsina, kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango yace gwamnan jihar Yobe Mai Mala Nuni zai ƙaddamar da hanyar Ingawa, Dutsi zuwa Shargalle.
Shi kuma gwamnan Sokoto Dr Ahmed Aliyu zai ƙaddamar da hanyar Yan Ɗaki, Shinkafi zuwa Kofar Soro a ƙaramar hukumar Katsina.
Sai gwamnan jihar kwara da zai buɗe kafafen makaranta na sakandare na musamman a garin Raɗɗa a karamar hukumar charanchi.
Haka kuma kwamishinan yaɗa labarai ya sanar da cewa gwamnati ta sanya ranar naɗa hakimai uku daga masarautar Katsina.
A cikin su akwai ɗa ga Gwamna Dikko Raɗɗa, Mohammed Dikko Raɗɗa sabon Hakimin garin Raɗɗa a ƙaramar hukumar Charanchi.
