Yara miliyan uku aka yi wa rigakafin cutar Polio a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Yara 2,954,362 yan ƙasa da watanni 59 da haihuwa aka yi wa riga kafin cutar Polio a shekarar 2025 a Katsina.

Shugaban hukumar bunƙasa harkokin lafiya a matakin farko Dr Shamsuddeen Yahaya ya bayyana haka a wajan taron ƙarawa juna sani da gwamnatin Katsina da haɗin gwiwa da UNICEF ta shirya a Katsina.

Taron da aka shirya kan gagarumin faɗakarwa gabannin gangami ƙaddamar da gudanar da allurar rigakafin cutar Polio a jihar.

Ya bayyana cewa a shekarar da ta gabata hukumar ta bi gida gida wajen gudanar da allurar Polio.

Dr Shamsuddeen ya ce ƙalubalen da suka fuskanta sun haɗa da turji daga wasu alummomi da yara da ba yadda ba a lokacin gudanar da rigakafin da sauran wasu matsaloli.

Ya ce gwamnatin Katsina ta shirya wajen gudanar da allurar rigakafin na shekarar 2026 domin tabbatar da nasarar a wannan shekara ta zarce shekarar da ta wuce .

Akan haka ne Dr Shamsuddeen ya bayyana cewa hukumar ta ɗauki ma’aikatan wuccin gadi 3,761 da za su bi gida gida da ma’aikata na musamman da kuma waɗanda za su tsaya a muhimmin wurere domin gudanar da allurar.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta tanaji allurar maganin miliyan 3,394,500 domin samun nasarar shirin.

Haka kuma ya sanar da cewa hukumar ta kaddamar da gangami da gudanar da majigi tare da amfani da gidajen rediyo wajan jawo hankalin al’ummar kan mahimmancin allurar rigakafin.

Sai ya yi kira ga manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki da su bada tasu gudunmawa wajen samun nasarar shirin.

By ukarofi