Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo ya koma APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Laraba ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa mai mulki, wato APC.

Hakan na ƙunshe a wani rubutu da ɗaya cikin ƴan gaba-dai-gaba-dai na APC mai suna Imran Muhammad ya wallafa ta shafin X a Jihar Kaduna.

Ana ganin Namadi Sambo ya yanke shawarar sauya sheƙa ne duba da rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP a mataki na jihohi da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Uba Sani na Kaduna, shi ne wanda ya karɓi Sambo bayan sauya sheƙar tasa a Gidan Gwamnatin jihar, ranar Laraba.

Namadi Sambo, shi ne mataimakin shugaban ƙasa a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Johnathan, daga shekarar 2010 zuwa 2015.

By Babaji