Gwamnoni, Ministan Tsaro da NSA sun yi taron gaggawa kan matsalolin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnoni daga jihohin Nijeriya sun taru a Abuja inda suke gudanar da zaman gaggawa game ta’azzara da lamarin taɓarɓarewar tsaro ke yi.

An yi taron ne a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) a sakatariyarta dake Abuja, wanda ya samu halartar gwamnoni da mataimakan gwamnoni daga jihohi 36 na ƙasar.

Duk da cewa ba a bayyana asalin abinda aka a tattauna a taron ba, ganin Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya nuna cewa matsalolin tsaro ne aka gina tattaunawar a kai.

Hakan na zuwa ne a yayin da kiraye-kiraye ya yawaita daga matakin hukumomin tarayya da na jihohi akan ɗaukar matakan daƙile ayyukan ta’addanci a sassan ƙasar.

Bayan kammala taron ne, wanda ya shafe sa’o’i uku, Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma yayin ganawa da manema labarai, ya ce suna shawarar kafa ƴan sandan jihohi bisa la’akari da buƙatar hakan da Gwamnan Jihar Benuwai, Hyacinth Alia ya gabatar.

Uzodimma ya kuma ce, za su cigaba da bai wa Shugaba Bola Tinubu goyon baya kan ƙoƙarinsa na warware matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

By Babaji