Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya bayyana haka a wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun sa.
Ya ce ‘yan bindigan sun shiga ƙauyen Rahamawa a garin Kuraye da ke ƙaramar hukumar Charanchi.
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigan sun sami nasarar awon gaba da Shanu guda 22 da raunana wani mutum mai suna Alhaji Ɗanmalam ɗan shekara 61 da haihuwa a ƙauyen.
Dr Nasiru Ɗanmusa ya bayyana cewa bayan samun bayanan sirri, jami’an tsaron suka bi sawun ‘yan bindigan har zuwa ƙauyen Dutsen Falale daidai iyakar ƙananan hukumomin Kurfi da Safana.
Bayan ɗaukar sa’o’i ana musayar wuta da yan bindigan, jami’an tsaron sun samu nasarar kashe ‘yan bindigan 12 tare da gano bindiga guda biyar ƙirar AK 47 da kuma ƙwato dabbobi 22 da suka sato a ƙauyen Rahamawa,inji kwamishinan.
Dr Nasiru Ɗanmusa ya sanar da cewa ‘yan bindigan sun kashe jami’in tsaro na sa kai tare da raunana soja guda ɗaya a yayin musayar wutar.
Jami’an tsaron sun haɗa da Sojoji, jami’an ‘yan sanda, jami’an tsaron al’umma CWC da yan sa kai.
Kwamishinan ya miƙa ta’aziya a madadin gwamnatin Katsina kan mutuwar ɗan bijilante da ya rasu .
Dr Ɗanmusa ya danganta nasarar da jami’an tsaron suka samu da irin mahimmancin da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta baiwa harka tsaro a jihar.
