Da alamu wasu na kan dutsen Arfa!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Haƙiƙa hawa arfa shi ne mafi girman ginshiƙin aikin hajji da in maniyyaci ya gaza halartar hawan a sashen wuni to ya rasa aikin hajji. Akwai wasu daga aiyukan hajji da za a iya gyarawa amma ban da Arfa. Ma’ana matuƙar mutum ya rasa Arfa to sai dai ya kara daura sabuwar aniya a shekara ta gaba ko a ce wani aikin hajjin don gudanar da aikin bias ƙa’ida. Abun da a ke sa ran mutum zai zama bayan ya sauko daga Arfa shi ne ƙara inganta imanin sa da taƙarƙarewa kan ibada don neman yardar Allah. Gabanin a hau Arfa akwai ibada da a ke yin a yawan salla da ma gabanin nan samun ziyartar Manzon Allah a Madina. In ka samu mai kwazo za ka ga ba ya rasa sallah a jam’i kuma duk rintsi ba zai share dare ya na sharer barci ba zai tashi ya yi kiyamul laili. Waɗanda kan shagala za ka samu sun maida masallatai wajen hira hatta ma ga waɗanda su ka samu shiga Raudhar Manzon Allah. Akwai ma masu shiga dandalin yanar gizo su na kale-kallen faya-fayen da ba su dace ba. Haka ne ma na ai in mutum ya hau yanar gizo ba yadda ya iya sai ya ga bidiyo ko hoton batsa da labaru na ƙarya. Wasu kuma sai ma su buga waya su na zantawa kan wasu lamuran na daban maimakon su taƙarƙare ga addu’o’i da nafila. A nan na ke son nuna mamaki ga wadanda na ke fargabar shin sun sauko daga Arfa ko har yanzu su na kan Jabalu Rahama? Dunƙulellen bayani ne da ke son hannun ka mai sanda ga waɗanda bayan sauka daga arfa amma ɗabi’un sa ba su sauya ba daga shagala zuwa maid a hankali ga ibada. Haƙiƙa akwai waɗanda a kan yi tashin hankali da su a wajen shiga mota har a nemi ba wa hamata iska. Aikin hajji fa na nunawa mutum hakuri da jurewa wajen ibada don a filin aikin hajji ba a faye tantance Sarki da Waziri ba ko sauran jama’ar ƙasa. Akasari maza kan sanya fararen mayafai yayin da mata kan sa hijaban su amma ba da nuna wani ado na zaman gida ba. Wato wannan wani misali ne na tashin alƙiyama. A kwanan Muzdalifa inda alhazai kan kwana a kasa ko kan ‘yan shinfudu da su ka sauwaƙa da hakan ke tabbatar da batun ba kullum a ke kwana kan gado ba. Idan mutum ya samu kan sa a wannan yanayi ai ya dace ya kara karatun natsuwa na sanin ɗan adam ba mai dauwama ba ne kuma duk wata darajar sa dai Allah ne ya halicce shi kuma akwai ranar da zai koma ga Allah ko ba jima ko ba daɗe. Girman kai rawanin tsiya ba shi da wani amfani a wajen mutum tun da an fito daga turbaya za a sake komawa turbaya. Babbar gata ce ga talikkai lokacin da Allah ya karɓi abun sa a samu yi mu su kabari a bunne da kasa. Don haka duk wanda zai kwanta kan kasa ba katifa ba iska bai dace ya ɗau kan sa gingim ba. A gaskiya na kan gamu da mutane a aikin hajji da kan fashe da kuka lokacin ibada da alamu ke nuna neman yafiya su ke yi daga zunubai da dacewa a gobe kiyama. Ba lallai kuma sai mutum ya fashe da kuka ne ke nuna juyayin sa ko miƙa wuya ga hukuncin Allah ba, Allah na duba zuciyar mutane ne. Niyyar mutum ita ce za ta fishshe shi. Hadisi na daya na Annawawi na ƙunshe da wannan saƙo da ke cewa dukkan aiki na tafiya da niyyar sa. Niyya kuma a cikin zuciya ta ke. Wani mawaƙi na cewa duk wanda ka ji a na cewa aniyar sa ta bi shi ya na ta faɗa aniyar ce ba ta da alheri har zuci. Wani mai jan hankali na cewa in da za a buɗe zuciyar wasu a duba ko a bayyana abun da ke can cikin zuciyar to ba ma za a iya zama da su ba don mugun nufi da su ke ƙunshe da shi. Shaidan kan matso daf da wanda ya ke gudanar da aikin hajji don ya kange shi daga samun cikakkiyar lada. Ya tabbata cewa ba wani sakamako da wanda ya samu karɓaɓɓen hajji zai samu a lahira sai aljanna. Wannan ya sa alkawarin da shaidan ya yi wa Allah cewa zai ɓatar da bayin sa sai waɗanda su ka tsaya kan imanin su kenan na tabbata a irin wannan yanayi. Ka ga har dai a ce akwai wani aiki da mutum zai yi ya ba shi aljannah to me zai hana duk wanda ya samu zuwa hajji ya dage ka-in-dana-in don cimma wannan babbar matsaya duk wuya duk tunzura mutum? Fushin nan faɗa mutum kan yi ba na ma yau da kullum ba ne, shaiɗan ne a makale ya na jira ya ga dama ko da ɗan ture mutum wani ya yi sai ka ga an nemi tada hatsaniya mai tsanani. Ba ma nan ma ba ka ga har wasu na neman tada tarzoma da sunan wani ya rike mu su wani haƙƙi alhali rashin haƙuri ne da buri mai yawa kan kawo haka. Idan har mutum ya samu kan sa a kasa mai tsarki don aikin hajji ai ya sallamar da komai ya fuskanci ibadar kuma ya jure har ya dawo gida lafiya. Bayan dawowa gida ma a ga mutum ya ɗore da ɗabi’u nagari hakan ke nuna alamun yiwuwar dacewa a aikin. Shin shiga ƙofar masallaci ne ko ma jiran layi don kama ruwa da ma layin karɓar abinci duk na iya sa mutum ya hasala, amma haƙuri da ɗaura niyyar lallai mutum zai jurewa duk ƙalubale zai taimaka ma sa wajen shanye wannan yanayi da ba sabam ba. Sayan tsaraba ba shi ne mafi a’ala a aikin hajji ba. Hakika na ga alhazan wasu ƙasashe na saya ko ɗaukar rowan zamzam da dabino a matsayin tsaraba. Ga alhazan mu na Afurka kuma musamman Nijeriya akwai sha’awar sayan kayan sawa da ma dan kunne ko sarkar zinari. Wasu ma mata da ma ƙalilan daga maza kan saka haƙorin bagwanja da ke alamta sun gudanar da aikin hajji. Duk wannan ba wajibi ba ne don shi aikin hajji rukuni ne cikin rukunai biyar na musulunci kuma ibada ce da a ke son mai guzuri, lafiya da kyakkyawar niyya ya gudanar da ita. Ba zan yi amfani da wannan damar wajen sukar masu sayan tsaraba ba matuƙar su na da halin yin hakan amma a duba abubuwa masu ma’ana ko da kuwa su na da tsada don sayen nagari maida kuɗi gida.

Labari daga Jabal Rahma bayan Arfa.

AN SAUKO DAGA ARFA YAYIN DA MUSULMIN DUNIYA SU KA YI IDIN BABBAR SALLAH

Masu gudanar da aikin hajjin bana sun sauko daga Arfa su ka kwana Muzdalifa inda su ka fara jifa yayin da miliyoyin musulmi da ke gida a faɗin duniya ke murnar Idin Babbar Sallah.

A ranar jifa ta farko JAMRATUL AƙABA an fito da yin jifar cikin zafin rana amma ba a samu wata barazana ta turereniya ba.

Jami’an tsaro su ka tsaya a duk sassan da a ke fargabar gamuwar mutane masu tafiya da masu dawowa don hana karo da juna.

Zuwa yanzu akwai karancin samun waɗanda su ka rasa ran su a sanadiyyar rashin lafiya kuma an tanadi wajajen karɓar magani.

Shugaban Hukumar Alhazan Nijeriya Sheikh Abdullahi Saleh Usman ya yi wa maniyyata fatan alheri a wata sanarwa daga jami’ar labarun hukumar Fatima Sanda Usara.

Yayin da a ke zama a tantunan Muna an samu gobara a gidan alhazan jirgin yawo da ke Makkah amma Allah ya taƙaita lamarin don bai shafi lafiyar kowa ba. Gidan na ɗaukar alhazai 484 inda tuni shugaban hukumar alhazan Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya ba da umurni a ka canjawa alhazan wani gida da ya cancanta da su. An ƙara inganta tsarin ciyar da alhazai abinci a masaukan su da hakan ya sa in ba dai mutum ya na da wara kwalama b ace to abincin zai wadatar da shi tun da ba a rasa nama da kaza. Ta kan kai ga wasu alhazan karɓar abinci fiye da buƙatar su da hakan ya ke jawo asarar abincin. Dibino da rowan zamzam ma manyan abinci ne da za su iya wadatar da mutum kafin ya dawo masauki ya zauna ya wanke hannu don cin tuwo da miyar kuka ko miyar da ta samu irin ta gida Najeriya. Abun bukata a nan gaskiya da riƙon amana a wajen ibada ta inda matuƙar mutum ya mayar da lamuran sa ga Allah zai samu biyan buƙatun sa na duniya da gobe kiyama.

KAMMALAWA

Wannan aikin Hajji shi ne karo na farko tun kafa Hukumar Alhazan Nijeriya ta NAHCON a 2006 da a ka damƙa ragama ga shehun malamin Islama Sheikh Abdullahi Saleh Usman ya jagorance shi. Dama ai aikin hajji na buƙatar malamai fiye da waɗanda a kan ɗauka don yin wa’azi. Shawara a nan a haɗa kai da malaman nan don gudanar da aikin bias ƙa’ida.

By ukarofi