Ɓarayi sun yi yinƙurin shiga gidan Ibrahim Gambari a Abuja

Spread the love

Daga FATUHU MUSTAPHA

Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da cewa ɓarayi sun yi yinƙurin shiga gidan Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari, da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja da subahin Litinin da ta gabata.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ce wannan yinƙuri ne mara kan gado da ɓarayin suka yi wanda ba su kai ga cim ma manufarsu ba.

A wani mai kama da wannan, Shehu ya ce a halin da ake ciki ‘yan sanda sun bazama neman wani ɓarawo ruwa a jallo wanda shi ma ya yi yinƙurin shiga gidan Maikano Abdullahi a Alhamis ta makon jiya.

A cewar Shehu, Maikano na da zama ne a layi guda da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da ke kusa da fadar ta Shugaban Ƙasa a Abuja.

Wata majiya ta ce faruwar wannan al’amari ya sanya Gambari da Abubakar Maikano da jami’in gudanarwa na ofishin Gambari ƙaurace ma gidajensu saboda tsaro.

Haka nan, majiyar ta ce ɓarayin sun yi awon gaba da kayayyaki gwargwadon hali daga gidajen biyu.

“An yi wa gidajensu fashi kuma ɓarayin sun ɗebi kuɗaɗe da wasu muhimman kayayyaki a gidajen biyu,” cewar wani ma’aikaci a ɗaya daga gidajen.

Bayanai sun nuna an bai wa Gambari wurin zama na musamman a gidan tsaro amma sai ya zaɓi ya zauna a Aso Rock kusa da Shugaban Ƙasa.

By Editor