Bagudu ya kama hanyar hana aukuwar haɗurran jiragen ruwa

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A matsayin wani mataki na hana aukuwar haɗurran jiragen ruwa a jihar Kebbi da kan yi sanadiyyar hasarar rayuka da dukiyo, gwamnan jihar Atiku Bagudu, ya ce za su duba su yi wa dokokin amfani da kan ruwa na jihar kwaskwarima.

Bagudu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Asabar ta hannun mai bai wa gwamnan shawara kan sha’anin yaɗa labarai, Malam Yahaya Sarki, a Birnin Kebbi.

Sanarwar ta nuna Bagudu ya yi wannan bayani ne sa’ilin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Yauri, Dr Muhammad Zayyanu a Juma’ar da ta gabata sakamakon mummunan haɗarin kwale-kwale da ya auku a yankin wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 160.

Gwamnan ya ce yi wa dokar kwaskwarima ya zama wajibi duba da yadda ake samun yawan aukuwar haɗarin jirgin ruwa tare da hasarar rayuka da dukiyoyi a jihar.

Sanarwar ta ce, “An sanar da gwamnan an gano gawarwakin mutum 76 daga cikin waɗanda haɗarin ya rutsa da su a yankin Warrah a Larabar da ta gabata. Sannan kawo yanzu an samu ceto aƙalla mutum 22 daga haɗarin.”

Kazalika, sanarwar ta ce 59 daga cikin gawarwarki 76 da aka gano dukkansu ‘yan garin Warrah ne. Tare da fatan a samu ceto ƙarin mutanen da suka rasa ransu.

“Haɗarin ya yi munin da har ya ja hankalin jama’a a ciki da wajen ƙasa, ciki har da Shugaba Buhari.

“Bagudu ya yi kira ga jama’a da su ɗauki darasi daga haɗurran da suka auku sannan su kauce wa aikata abin da ka iya jefa rayukansu cikin hatsari”, in ji sanarwar.

Mai bada shawara game da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Alhaji Sani Dododo, a madadin gwamnatin jihar ya bada sanarwar tallafi na kuɗi Naira milyan N11 ga ahalin waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata da ma waɗanda suka yi hidimar bada agaji a haɗarin.

By Editor