Ɓatanci ga Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam): tsumagiyar kan hanya!

Spread the love

Daga FATUHU MUSTAFA

Da farko dai ya kamata a sani, musulmi a Arewacin Nijeriya ba son Annabi Muhammad (SallalLahu alaihi wa sallam) kawai suke ba, baya ga soyayyar ma, ba wani mahaluki da suke ganin girma kamar Sa. A iya sanya imaninsu a matakin hadisin nan da yake cewa, “imanin ɗayanku ba ya cika, sai ya so ni fiye da iyayensa, da dukiyarsa da iyalinsa”. Maganar gaskiya in har kana so ka ga fushin musulmi a Arewa, to ka taɓa mutuncin Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam), yanzu za ka iske huzni a tare da su, da ba ka tava gani a rayuwarka ba.

Ko shakka babu, wannan mata ba ta kyauta ba, ta kuma keta hurumin dukkan musulmi da take zaune a cikinsu. Kuma ya zama wajibi a ɗauki mataki na shari’a a kanta. A irin fahimtar da na yi wa abin, ban ga alawar Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) da abinda ya faru a guruf ɗin wasaf na ‘yan makarantarsu ba. Don haka, ba ta da wata hujja ta sanya Shi a cikin maganar, balle ma har ya kai ta gaya masa irin waɗannan baƙaƙen maganganu. Mu dai musulmi ya kamata su kiyaye, mu mutunta addininmu. Idan an kafa guruf don sha’anin Duniya, to a tsaya a sha’anin Duniya. Idan an kafa shi don sha’anin lahira, to a tsaya a sha’anin lahira.

Amma babban abinda yake ba ni tsoro a kan wannan ɗabi’a tamu ta ɗaukar doka a hannunmu ita ce, idan ba a yi hankali ba, nan gaba za mu zamo kowa zai iya kashe mutum ya ce “Annabi ya zaga”. Ya kamata mu sani, musulunci addini ne mai tsari. Babu wani lokaci da musulunci ya yarda kowa ya ɗauki doka a hannunsa. Abinda ya tabbata shi ne, idan ka kama mutum da laifi, ka gabatar wa sharia shi, ita kuma shari’a ta bincika ta tabbatar, sannan ta yanke masa hukuncin da ya dace.

Wani abin kuma shi ne, a ƙasar nan muna da wakilai a kowanne mataki na gwamnati. Tun daga ƙananan hukumomi har zuwa tarayya, da za mu iya sanyawa a sanya wannan hukunci ya zama doka. Ko da a matakin jiha ne kuwa, jihohinmu za su iya kafa waɗannan dokoki. Babban dalilin da ya sanya ɗaliban makarantar Shehu Shagari suka ɗauki wannan doka a hannunsuna hukunta La’ananniyar da ta yi wannan aika-aika shi ne, na tsoron da suke dokar ƙasa ba za ta hukunta ta ba. Musamman ganin yadda aka baiwa ‘yar Jaridar nan ta Thisday kariya, a yayin da ta yi izgili ga Manzo Allah (SallalLahu alaihi wa sallam). Ya kamata a ce tun daga wannan lokaci, gwamnonin jihohin musulmi su kafa dokar hana irin wannan a jihohinsu. Deborah ta yi abinda ta yi ne, saboda ta yi imanin ba dokar da za ta hukuntata a Nijeriya don ta yi haka. Su ma da suka kashe ta, sun kashe ta ne, saboda sun san ba wata doka da za ta hukuntata a tsarin ƙasar nan.

Amma dai magana ta gaskiya, hanyar da suka bi wurin kisan, bai dace da koyarwar addinin Musulunci ba. Musulunci bai yarda da irin wannan tsari ba, saboda zai haifar da ɗan da ba ido, ko da kuwa a tsakanin musulmi. Ina ga ya kamata a nuna wa musulmi muhimmancin yin komai a hukumance. Hakan shi ne abu ma fi alheri a gare mu.

Allah ya ƙara mana so da ƙauna da biyayyar Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam)
Fatuhu Mustapha ƙwararren ɗan jarida ne. Ya rubuto ne daga Abuja.

By Editor