‘Yar wasan barkwanci Helen Paul ta zama Farfesa

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Sananiyya kuma sharararriya a fagen nishaɗantarwa Helen Paul, ta kafa tarihi a duniyar barkwanci ta hanyar zama ‘yar wasan barkwanci ta farko a Nijeriya da ta fara zama farfesa.

Idan ba mu manta ba, a ‘yan kwanakin baya ne ta samu kammala digirinta na uku a ɓangaren wasan kwaikwayo wato Theatre Arts a jami’ar Iko.

Halen ta bayyana wannan ne a shafukanta na sada zumunta. Ta kuma ƙara da taya mijinta murna kan tasa nasar ta zama dakta a vangaren karatun lauya(Doctor of Law) duk dai a jami’ar ta Iko.

“Ina taya dukka ɗaukacin ‘ya’yan jami’armu. A yanzu na zama cikakkiyar farfesa, Farfesa Poul Helen. Taron qaddamarwar ya cika taro matuƙa. Godiya ta musamman ga ubangidana kuma shugaban jami’ar, Dornett Mcintosh Ph.D,”inji Helen.

Ta ƙara da cewa, “ina miƙa godiyata ga babban malamina Farfesa Cox. Ba zan tava mantawa da Yesimi Dunmoye a jerin sunayen waɗanda na ke miqa sakon godiyata ba, shugabar shirye-shirye ta jami’ar.”

Baya ga wannan nasara, an naɗa Poul Helen a matsayin shugabar Shashen Fasaha, Kiɗa da Nishaɗi ta jami’ar Heart International ta Ƙasar Amurka.

By Editor