Mawaƙa biyar da alburushi ya yi sanadin mutuwarsu

Daga AISHA ASAS

Kamar yadda muka sani, a cikin kowacce sana’a akwai ƙalubale da kuma haɗuwar da ke cikinta. Duk da cewa wasu na ganin ba abin da zai iya samun su ta ɓangaren yanayin sana’ar su, kasancewar sana’ar mai cike da kwanciyar hankali, wadda ba ta jawo rigima bare har ta kai ga hatsaniyar da ka iya zama barazana ga rayukansu.

Sana’ar finafinai dai na ɗaya daga cikin irin waɗannan sana’o’in da ake ganin ba tashin hankali a cikinta, sai ma dai nishaɗantar. Sai dai a tawa fahimta, ba inda za a rasa barazana a cikin al’umma matuƙar akwai zuciyoyin da suke yi wa shaiɗan bauta.

Hassada na ɗaya daga cikin manyan makamai masu saurin tasiri da ke iya kai wa ga hasarar rayuka ko da kuwa ido bai hango hakan ba. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da aka rasa dalilin yawaitar kashe-kashe a tsakanin masana’antun finafinai da aka sani da so da ƙaunar juna musamman ma na ƙasashen waje.

A yau za mu kawo kaɗan daga cikin waɗanda aka yi wa kisan gilla ta hanyar harbe su da bindiga, duk da cewa suna da yawa, sai dai za mu kawo biyar ne kawai daga cikin su:

Idhu Moose Wala: Ɗaya daga cikin mawaƙan Punjabi da Ƙasar Indiya ke so da yawan sauraren waƙe-waƙen sa, ya zama ɗaya daga cikin mawaƙa da alburushi ya aika lahira.

Wala

Mutuwar ta sa kuwa da zafinta, domin a satin da ya gabata ne na sa wa’adin ya cika, inda ake zargin ɗan daba Lawrence Bishnoi da aikata wannan aika-aika ga sananne kuma matsahin mawaqi mai shekaru 28 da haihuwa, wato Idhu Moose Wale.

Scott La Rock: Scott Monroe Sterlin, wanda aka fi sani da La Rock, mawaƙin gambara ne na Ƙasar Amurka. Mawaƙi ne da ya shigo harkar da ƙafar dama, domin ya yi nasarar kaiwa wurin da dayawa da suka jima ba su samu damar isa ba. An ruwaito cewa, mawaqin ya samu kwantaraki da shahararren kamfanin waqa da duniya ke ji da shi Warner Brothers Records wanda hakan kawai nasara ce ta a zo a gani.

Scott

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa, albom ɗin La Ruck na farko na cikin ganiyar sa, yayin da mutane ke ta ribibinsa, har ya fara tsallen nasara don isa jerin mafi shahara da duniya ta san da zaman su ne mutuwa ta yi masa tsaiko. Scott ya gamu da ajalinsa ta sanadiyyar ɗana masa alburushi da wani ya yi da ya yi sanadiyyar baquntar sa lahira a ranar 13 ga watan Yuli, shekara ta 1987.

Tupac Shakur: bana jin Tupac na buƙatar gabatarwa ga ma’abuta sauraren waƙoƙin turanci, dalilin shahara da sunan da ya yi.

Tupack

Ya kasance a jerin mawaƙan da duniya ta kira da suna qwararru. Duk da cewa yanayin waƙoƙin Tupac sun fi da bayyana qunci ko ta’addanci, hakan bai sa aka yi zaton ganinsa a jerin waɗanda za a gani a wannan layin ba, domin tuni masoyansa suka ɗaura waƙoƙin na sa a mizani, suka auna, inda suka tsaya akan ƙurciyarsa ce yake bayyanawa a cikin na sa salon. An kashe Tupac Shakur ne a cikin motarsa, yayin da yake tuƙi, a garin Las Vegas, shekara ta 1996.

Young Dolph: mawaƙin da aka ɗura wa jikinsa alburusai 22 a lokacin da ya je siyo wa mahaifiyarsa biskit a kantin da yake yawan zuwa. An harbe Young a shekara ta 2021.

Dolph

Notorious BIG: Cristopher Wallace wanda aka fi sani da Notorious Big ya gamu da ajalinsa ne a shekara ta 1997, watanni shida cir da kashe Tupac. Ya mutu ne a yayin da mahara suka buɗa masa wuta, a lokacin da yake jiran wutar tirafik ta ba shi damar wucewa.

BIG