Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gidauniyar Kannywood da haxin gwiwa da hadaɗiyyar Ƙungiyar masu Shirya Finafinai ta Ƙasa, MOPPAN da hukumar da ke kula da cuta mai karya garjuwar jiki, wato SAKA, ta shirya gangami a kan ranar tunawa da cuta mai karya garkuwa ta HIV a ranar 1-12-2022.
Gangami wanda ya fara da tattaki daga Ƙofar Nasarawa zuwa gidan Makama, inda daga nan aka garzaya ɗakin taro na Kannywood TV da ke unguwar Tudun Yola,
Tun da farko a jawabinsa Dr. Ahmad Muhamad Sarari, wanda shi ne Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Shirya Finafinai ta ƙasa, ya bayyana cewa, sun shiga cikin wannan gangami wayar da kai ne domin faɗakarwa da jan kunnen al’umma akan wannan cuta mai karya garkuwa ta AID.
Ya ƙara da cewa, “muhimmacin Kannywood ne ya sa muka shiga cikin wannan gangami domin idan ka duba Kannywood tana kowanne gida, kuma tana kowanne saƙo da lungu, kuma idan ka ɗauki ‘social media’ dan Kannywood zai iya aika saƙo cikin minti biyu zuwa uku, mutum Miliyan 10 saƙon ya je masu, kuma cikin hikima da basirar da za ta ja hankali, kuma da ma ita Kannywood tuntuni ta yi nisa wajen yin finafinai da suke faɗakar da al’umma akan wannan cuta kamar su ‘Waraka’, ‘Jankunne’, ‘Tsalle Ɗaya’ da sauransu.”
Shi ma a jawabinsa, Dr. Nura Abubakar, wanda shi ne babban Jami’in Hukumar kula da Cuta mai Karya Garkuwar Jiki ta Jihar Kano, ya ce, maƙasudin tunawa da ranar ta 1-12- 2022 shi ne, a bai wa masu ɗauke da wannan cuta gudunmawa, a tuna da waɗanda suka rasa rayukansu sanadiyyar wannan ƙwatar cuta, sannan a wayar wa da ja’ama kai akan muhimmancin zuwa gwaji da faɗakarwa akan rashin nuna ƙyama ga waɗanda suka kamu da cutar.

Sannan ya ce, “Ina kira ga al’umma da su je a gwada su, don sanin matsayin mutum ya je a gwada shi, don sanin yana da ita ko ba shi da ita. Mai ita a ɗora shi akan magani, domin rashin karɓar magani yana ƙara yaɗuwar wannan cuta a cikin al’umma.”
Daga karshe dai an raba takardun shaida ga waɗanda suka halarcci sanin makamar aiki da ya gudana tun a ranar 2 zuwa 6 ga October 2022.
Gangamin da lakca dai ya samu halartar jiga-jigan a masana’atar Kannywood maza da mata.
