Me ke kawo taƙaddama tsakanin surukai a ƙasar Hausa?

Daga AMINA YUSUF ALI

Masu karatu sannu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan mako muna tafe da bayanai a kan yadda alaqar tsakanin surukai take ƙara lalacewa a ƙasar Hausa har take zama ma kamar kishi ne tsakaninsu ba wai surukuta ba.

Wannan abu ne mai matuar ban mamaki musamman idan muka yi la’akari da yadda alaƙar surukai take jiya a ƙasar Hausa. A zamanin da, ba komai sai kunya da tsakanin surukai a ƙasar Hausa. Kuma mafi yawan lokuta ma a gida guda suke zaune. Amma hakan bai sa ko da wasa suruka ta nemi raina uwar miji ba. Haka ita uwar mijin ba ta yarda surukar ta raina ta ba. Amma a yanzu abu ya koma har suruka ta mari suruka wani sa’in ma ka ga suna jefa wa juna baƙaƙen magana har ma da habaici kamar wasu kishiyoyi.

Ba shakka wannan mataki ne da ya zama baƙo a ƙasar Hausa. Haka ɓangaren maza ma ba a bar su a baya ba. Domin su ma sun canza ɗabi’unsu daga yadda aka san surukai a ƙasar Hausa suna girmama iyayen matansu. Yanzu abun kam sai godiyar Allah. Domin abin ya kai ka ga ana sa’insa tsakanin surukai. Abun ko kyawun gani babu. Musamman idan savani ya shiga tsakaninsa da ‘yarsu an nemi a yi masa faɗa ko gyara. Duk da dai akwai ƙananan mutane waɗanda ba sa jan girmansu a wajen surukansu. To laifin wanene? A binciken da muka yi, mun gano wasu dalilai kamar haka:

Dalili na farko, wasu suna ganin tun ran gini tun ran zane. Kuma kowa ya sayi rariya ya san za ta masa asarar ruwa. Wato ma’ana da ma dukkan surukan da suke cin mutunci ko raina juna da ma can ba mutanen kirki ba ne masu mutunci ba. Da ma taron marasa tarbiyya aka haɗa a dukkan ɓangarorin. Don gaskiya mutanen kirki masu mutunci ba za su aikata hakan ba.

Dalili na biyu kuma, wasu suna ganin yadda aka yi watsi da al’adun Hausawa masu kyau. Saboda shigowar zamani da wayewa da cuɗanya da baqin al’adu da wasu sababbin fatawoyi daga wasu malamai dukkansu sun bayar da gudunmowa babba. Yanzu wayewar zamani ta zo ana ganin waccan kunya da ake ji tsakanin surukai tamkar gidadanci ne da rashin wayewa. Wasu kuma suna ganin burgewa ce a daina wannan kunyar.

A da suruki yana matuƙar jin kunyar iyayen matarsa. Haka ita ma matar tana tsananin jin kunya da nauyin nasa iyayen. Ba za ta tava ƙetare maganarsu ba. Wata ma ko unguwa za ta je sai dai ta tambayi iyayen miji ba dai mijin ba. Haka a ɓangaren mijinta ko ido bai iya haɗawa da nata iyayen saboda tsananin jin kunya da nauyinsu. Yana girmama su tamkar iyayensa. Ko mai sunansu ya ji ba ya iya maimaitawa. Sai dai ka ji yana cewa, mai sunan Baba haka. To su kuma iyayen ba haka kawai suka samu girman nan ba. Su ma sun taka rawa ta kyautatawa da haƙuri da juriya da kau da kai. Suna nuna wa surukai so fiye ma da nasu ‘ya’yan. Ba tsangwama bare kishi. Idan savani ya samu tsakanin ma’aurata akan haɗu a gyara. Saɓanin yanzu da ake fito-na-fito kowa ya goya wa nasa baya. Inda daga ƙarshe sai a rabu baram-baram dutse a hannun riga.

A zamanin da ba a tattauna shirye-shiryen aure da uwar amarya. Mafi yawancin lokuta da ‘yar uwarta ko kishiyoyinta ake shiga a yi komai da su. Amma yanzu sai ka ga uwar Amarya da Ango kullum ita kenan waya da shi tana tambayarsa yadda za a yi biki. Wani sa’in ma ita ke tambayar kuɗaɗen al’ada kamar lalle da gyaran jiki da sauransu. Tun daga nan za ta yi abinda sakin jikin zai yi yawa har ma raini ya shiga tsakani.

Haka wajen al’adun biki. Yanzu dina (Dinner) ta riga ta zama ɗaya daga cikin bukukuwan da ake yayin aure. Haka kamu an zamanantar da shi ta yadda iyaye mata da ma angwaye za su halarta. A yayin waɗancan shagulgula ango kan fito ya yi rawarsa a gaban iyayenta, ita ma Amaryar takan fito ta yi a gaban nasa iyayen. Haka uwar Ango ma kan yi rawa a gaban iyayen matar, haka dai. Tun daga nan fa abubuwa kan lalace. To sai ka ga Ango bai daraja surukansa yadda ya kamata.

Dalili na uku shi ne, su kansu yaran ba sa girmama iyayensu yadda ya kamata shi ya sa har surukan suke samun ƙofar raina iyayensu. Wato dai abinda Hausawa suke cewa, wai sai bango ya tsage sannan ƙadangare yake samun damar shiga. To idan namiji ba ya girmama iyayensa matar tana kula. Kuma ita ma haka za ta dinga yi musu rashin ladabi. Wani namijin ma har qorafin uwar yake yi a wajen matarsa ta fiye kaza-kaza. Wanda sam wannan bai dace da ɗabi’a ko al’adar mutanenmu ba da kuma tsarin tarbiyya. Haba ɗan’uwa! Wannan matar da ka aura jiya ko shekaran jiya har ta fiye maka mahaifanka da kuke tare tun bara da bara waccan? Har kun qulla amincin da za ka dinga kawo mata sirrin iyayenka. Hakan sam bai kamata ba. Kuma yana buɗe ƙofar raini tsakaninsu da ita.

Haka su ma mata a ɓangarensu, tun lokacin da namiji ya zo neman aure kike nuna masa iyayenki ba su da ƙima a wajenki. Kuma da zarar ya ɗau wannnan karatun, to wallahi ke ma kin kaɗe har ganyenki. Ba yadda za a yi ya raina iyayenki ke kuma ya ƙimanta ki ba. Wata ki da zance ya zo ba ta son ta nuna gidansu na gaskiya. Saboda iyayenta talakawa ne. Gani take ajinta zai zube idan ya fuskanci haka. Amma abin la’akari fa shi ne, namiji matuƙar yana sonki ko da kin fi veran masallaci talauci ba ruwansa. Gara ma ki fito fili ki nuna gaskiya idan ya ga zai iya ya aura, idan ba zai iya ba, ya ƙara gaba.

Dalili na huɗu shi ne, rashin kunya. Ko da manya sun zubar da girmansu, wani lokacin ai ana duba surukuta a raga musu. Mata da maza marasa kunya su suke wulaƙanta surukai. Ba sa kau da kai a kan abinda suke aikatawa a kansu saboda albarkacin auren da ya gifta a taakaninsu.

Dalili na biyar kuma shi ne, Sa ido. Haƙiƙa rashin kau da kai a kan komai ma matsala ce a rayuwar nan. Wannan ya fi faruwa tsakanin surukai mata. Duk macen da take sa ido a kan abinda mijinta yake wa danginsa ko mahaifiyarsa ta ɗauko wa kanta Dala da Goron Dutse dukka ba gammo. Domin kuwa za ta yi ta wahala a kan abinda ba ta isa ta hana ba.

Domin uwar nan tasa tare kika gansu. Ita ta yi ɗawainiyarsa har a zama mutum kika gani kika yi sha’awa, har kika aura. Meye naki na kishi da ita? Ko so kike ki jefa shi a wutar Allah ta hanyar saka shi ya juya mata baya? Ki tuna ke ma za ki haifa. Kuma ke ma watarana uwar miji ce. To ya za ki ji idan hakan ta faru a gare ki? Haka ke ma uwar miji ya za ki ji idan aka maimaita abinda kike yi wa ‘yar mutane a kan naki ‘ya’yan ko na ‘yanuwanki?

Haka ita ma uwar miji akwai mai sa ido wacce ba ta ƙaunar ɗanta ya mora wa iyalinsa ko biyar. Ita a wajenta wannan surukar ita ce kishiyarta. Wata ko ɗaki ta tsani ta ga ɗanta da matarsa sun shiga. Sai kishi ya turnuqe ta. Wata ko kwalliya da girka masa abinci tana gasa da suruka. Haba Hajiya, ai tun daga haka kin buɗe wa kanki ƙofar raini. Sai an samu suruka mai tarbiyyar gaske ce za ta girmama ki da wannan halin.

Dalilina na shida shi ne, rashin amfani da koyarwar musulunci da rashin tsoron Allah. Da a ce Surukai za su ji tsoron Allah su zauna da juna bisa koyarwar musulunci da an huta. Ita suruka ta sani, ba ki da hurumin hana mijinki yi wa Uwarsa ɗawainiya. Haka ke ma uwar miji ki sani, hana ɗanki yi wa matarsa ɗawainiya halakar da shi ne. Matarsa na da haƙƙi kamar yadda ke ma kike da shi.

Hana shi yi musu hidima. Ko kuma ki ce sai dai duk abinda za ta saya yana hannunki. Haka ko da kuɗin cefane ne, sai dai a karɓa a wajenki. Gaskiya ba ki saya wa kanki mutunci ba. Kuma idan ‘yarki aka yi wa a gidan miji sai ki ce ba ki yarda ba. Bayan musulunci ya koyar da mu so wa junanmu abinda muke so wa kanmu.

Haka kai ma suruki mai burin yi wa surukai wulaƙanci saboda ka ga ka fi su arziki. Musulunci ya koyar da mu girmama na gaba da kuma tausayin na ƙasa. Kauce wa hakan ba zai haifo ɗa mai ido a gare ka ba. Allah ya sa mu dace. Za mu ci gaba a mako na gaba idan Allah ya kai rai.

Da fatan za ku cigaba da karatun jaridarmu mai farin jini ta Blueprint Manhaja.