Halin da sakatariyar Kebbi ke ciki bayan shekaru 10 da fara aikinta kan biliyoyin Naira

Daga AMINU AMANAWA a Kebbi

“Na kan kashe kusan dukkanin albashina wajen tafiya aiki da samarwa kaina muhalli da abinci, saboda nisan wajen da nake aiki. Ka ga Ina ƙarƙashin Ma’aikatar Kasafi tana nan cikin Birnin Kebbi, amma sashen da nake na Bagudu tafiyar kilomita 160 zuwa 200, wanda ba zai yiwu na je aiki kullun na dawo ba, abinda ya sa albashin da nake karva ba ya isa ta ɗawainiyar tafiya kawai, da abinci da wurin zama dole sai  na ɗan haɗa da ɗan buge-buge, saboda ba muhalli, kuma maganar gaskiya indai mahalli ne ko manyan sakatarori ba su da shi, indai a Kebbi ne, balle sauran ƙananan ma’aikata.”

Usman Muhammad Anache, ɗaya daga cikin ma’aikatan gwamnatin Kebbi ke nuna damuwarsa kan yadda warwatsewar ma’aikatu da ma sassa ke laƙume albashin ƙananan alhaki wajen ƙoƙarin sauke nauyinsu na aiki.
“Maganar gaskiya rarrabuwar ma’aikatu daban-daban a cikin Birnin Kebbi ya shafi yadda muke gudanar da ayukkanmu a matsayinmu na ma’aikata, musamman ɓata lokaci wajen aiwatar da ayukkan gwamnati da ma tafiyar da su.

“Misali Sakatariyar Gwadan Gwaji tana ɗauke da Ma’aikatar noma da kiwo, amma Karda da Cascom da suke ƙarƙashin ma’aikatar suna Kalgo, ka ga ko aiki ake son yi tsakanin kwamishina na noma da kiwo da Janar Manaja na KARDA, ko KASCOM, ka ga abin zai ɗau lokaci ko an ce wannan zai yi signing ɗan tsakanin nan Gwadan Gwaji Sakatariya zuwa KARDA ya fi kilomita 10 saboda sai ma ka fita daga ƙwaryar birnin Kebbi.

“Ga ma wani misali Ma’aikatar ba da ilimin bai ɗaya  itama tana nan a Gwadan Gwaji amma SUBEB tana can hanyar barikin soji ka ga nisan ya kai kilomita 6.

“Ita ma Ma’aikatar muhalli tana Bulasa kuma nisan zai kai 5 kilomita, amma ma’aikatar kula da dazuzzuka tana nan kusa da gidan Gwamnati. Ka ga ko da gwamnati ɗa ta ce samar da motoci dan wannan sufurin a nan Kebbi ba zai yiwu ba, saboda dukka ministry da hukumomi warwatse suke cikin Birnin Kebbi.

“Ka ga idan ka ce ka xauki ma’aikatan Karda ka kai su Kalgo, ka zaga yo, ka ɗauko ma’aikatan Kuda, zuwa titin Emir Usman Haruna road, ka zo Tudun wada da sauransu ka ga ba zai yu ba.

“Ita ma Ma’aikatar Shari’a tana nan kusa da gidan Gwamnati. Ita ma Ma’aikatar lafiya tana Gwadan Gwaji amma wasu department ɗinta nan titin Emir Haruna kusa da CBN. Haka ma ma’aikatar ilimi ta Gwadan Gwaji. Amma hukumar makarantun sakandare na wannan hanya ta titin Emir Haruna road kusa da gidan Sule ba Saura. Su kuma ma’aikatun makarantun gaba da sakandare da ta ayyuka suna ƙarƙashin Halliru Abdu road,” inji shi.

A Shekarar 2012 tsohuwar gwamnatin gwamnan wancan lokacin, Alhaji Saidu Usman Nasamu Ɗakin Gari, ta bayar da kwangilar samar da sakatariyar kan kuɗi Naira biliyan 3.8. Aikin dai a lokacin ya ƙunshi samar da ginin ofisoshi da zai iya ɗaukar ɗawainiyar kusan dukkanin ma’aikatun jihar, da ofishin shugaban ma’aikata na jiha, da na sakataren gwamnati baya ga masallatai, wurin cin abinci da dai sauransu.

Yunqurin samar da sakatariyar dai ya biyo ne bayan rarrabuwar ma’aikatu daban-daban dake cikin ƙwaryar birnin na Kebbi baya ga waɗanda ke akwai a Gwadan Gwaje.

Sai dai yayin da aikin ya kai kashi 50 na matakin kammaluwa gwamnatin a Nuwambar 2014 ta sake sabunta kwangilar aikin zuwa Naira biliyan 7 da ɗoriya, aikin da ya cigaba da tafiyar hawainiyar har zuwa lokacin da gwamnan jihar mai ci yanzu Abubakar Atiku Bagudu ya sake sabunta aikin kwangilar a karo na biyu.

Wannan ko ya biyo bayan buƙatar sake duba aikin kwangilar da kamfanjin dake aikin na RockWell Development Nig LTD. (Kamfanin ‘yan chana) lamarin da ya sa gwamnatin jihar watsi da wannan buƙatar.

Kabawa sun nuna damuwa:

A shekarar 2019 ɗimbin masu kishin jihar Kebbin ne suka rika fitowa a kafafen sada zumunta na zamani, inda suke nuna damuwa kan watsi da aikin na gina sakatariyar.

Yayin da wasu ke dasa ayar tambayar kan cewa, ko me ya sa gwamnatin da ta fito da aikin kasa kammala shi? suna masu cewar bai kyautu ba a ce gwamnati ta fito da aikin da ba ta iya kammalawa.

Bagudu ya fitar da kuɗi domin kammala aikin:

Sai dai a shekarar 2020 gwamnatin jihar mai ci yanzu ƙarƙashin jagorancin Abubakar Atiku Bagudu, ta amince da fitar da naira miliyan N949,198,886.26, domin ba wa kamfanin Rock Well Development Nig LTD ya samu damar kammala aikin ginin sabuwar sakatariyar Gwadangaji dake Birnin Kebbi.

A wani bayani da mai magana da yawun gwamnan Abubakar Mu’azu Ɗakingari ya fitar, ya Ambato kwamishinan ayukkan Alhaji Abubakar Chika Ladan na cewa fitar da kuɗin ya biyo ne bayan cimma matsaya da gwamnatin ta yi da a cewar kwamishinan aikin idan an kammala shi zai tallafa matuƙa wajen gudanar da ayukka a Kebbi.

’Yan Jiha na nuna damuwa:

Shehu Isa S/Kudu wani mai fafutikan cigaban jihar Kebbi ne, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan watsi da aikin, duk kuwa da cewa an warewa aikin maƙudan kuɗaɗe domin kammala shi.


“Ya kamata a ce gwamnatin Kebbi ta cire duk wani abu, ta zo ta kammala aikin nan, sa’ilin da saura ke cigaba da kasancewa a hannun rabbu ka wadata mu, ka duba gwamna Atiku Bagudu ya amince da fitar da sama da Naira miliyan 900 domin kammala aikin, amma ka duba har yanzu aikin shiru kake ji tamkar an shuka dusa”

“Maganar gaskiya kuɗaɗen nan da aka fitar sun isa a ce an kammala wannan aikin dama dangoginsa, sai dai a maimakon haka, gwamnati ta cigaba da bayar da sababbin kwangiloli a zaman majalissar zartaswa.” 

Shehu S/Kudu hakama ya yi zargin cewa, wannan abun damuwa ne, kuma abin Allah wadai a cewar sa.

Ko me ya kawo tsaiko ga kammala aikin?

A zantawa ta musamman da na yi da kwamishinan ayukka na jihar Kebbi Alhaji Abubakar Ladan kwamishinan ya zargi kamfanin dake aikin da kawo tsaiko ga kammaluwarsa, kasancewar kamfanin ya kasa komawa bakin aikin duk kuwa da maƙudan kuɗaɗen da aka ware masa.

“Kamar yanda ka sani wannan aikin gwamnati mai ci yanzu ta gaje shi ne ga tsohuwar gwamnati da ta ba da kwangilar yinsa tun a shekarar 2012 kan tsabar kudi Naira biliyan 3 da ɗoriya, wanda daga bisani ta sake sabunta kwangilar aikin zuwa naira biliyan 7.7 wato kusan dai kaso 100 na adadin farko da aka samo kwangilar.”

Sai dai bayan shigowar gwamnatinmu, mai girma gwamna ya cigaba da aikin sabunta kwangilar da sama da Naira miliyan N900 da manufar kammala aikin, sai dai ‘yan watanni da cimma matsaya da kamfanin ya kasa dawowa domin cigaba da aikin, bayan buƙatar sake sabunta kwangilar a karo na biyo abinda gwamnatinmu ta qi, saboda mun lura cewa kuɗin da aka samar wa kamfanin sun isa kammala aikin, kwatankwacin kuɗin da aka samar domin gina asibitoci, makarantu da dai sauransu.

“Saboda haka, muna shawartar kamfanin da ya zo domin cigaba da aikin, abinda ya qi kuma muna kan wannan matsalar.”

Don haka, idan kamfanin ya kasa komawa domin cigaba da aikin, za mu duba daftarin da tanadin dokoki domin mu ga mai doka ta ce idan buƙatar soke kwangilar ce mafita za mu yi, ko samar da kamfanin da zai iya kammala aikin.

“Aikin ba ƙarami ba ne, yana da matuƙar muhimmaci, ka ga ko nan ma’aikatar ayukka muhallinmu makarantar sakandare ce  baya, da muka mayar a Jega domin mayar da wannan wajen muhallinmu, amma insha Allah za mu kammala aikin kafin ƙarshen wa’adin mulkin gwamna Bagudu.

Me kamfanin Rock Well ke cewa?

Duk ƙoƙarin da na yi niyyar jin ta bakin kamfanin abu ya ci tura, sai dai a wata zantawa da kakakin kamfanin dake Kebbi Muhammad Shehu Nasir ta  wayar tarho, kakakin ya shaida min cewa lallai kamfanin ya tattara nasa ya nasa ya  bar jihar, kasancewar gwamnatin jihar ta kasa sake sabunta kwangilar kamar yanda suka nema a karo na biyu saboda hauhawar farashin kaya, a cewarsa.