Ina da burin kawo canji a siyasar Filato ta Arewa – Hon. Sahlan

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos

Shiyyar Filato ta Arewa daga Jihar Filato yanki ne da ya daɗe yana shan gwagwarmaya da rikita-rikitar siyasa, saboda kasancewar sa yanki mafi yawan jama’a da tarin albarkatun ƙasa, ƙabilu nabambanta, wanda kuma ya sha fuskantar hare-hare da rikice-rikice masu nasaba da siyasa, ƙabilanci da addini. Har wa yau kuma shi ne yanki mafi kusa da gwamnatin tsakiya mai hedikwata a Jos, Babban Birnin Jihar Filato.  Hon. Muhammad Shafi’u Yakubu Sahlan na daga cikin matasan ‘yan siyasar da suka fito zawarcin kujerar Sanata da zai wakilci Shiyyar a Majalisar Ƙasa.  A zantawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, Hon. Shafi’u Sahlan da ake yi wa laƙabi da Sahlaniyya, saboda karɓuwarsa a wajen jama’a musamman mata da matasa, ya ce idan har Allah ya ba shi nasara a wannan takara da yake yi a ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP zai kawo sauyin da zai bunƙasa rayuwar al’ummar yankin baki ɗaya.

MANHAJA: Yallaɓai, ko za ka gabatar mana da kan ka?

Alhamdulillahi. Ni suna na Hon. Yaqub Muhammad Shafi’u da aka fi sani da Sahlan. Kuma ni ne ɗan takarar kujerar ɗan Majalisar Dattijai a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar NNPP. Ni ne kuma shugaban makarantar koyar da aikin jinya da kiwon lafiya ta Sahlan School of Health Technology da ke nan Jos, da sauran rukunin makarantun Sahlan na boko da na addini. 

Ko za ka gabatar mana da tarihinka a taƙaice?

Ni haifaffen garin Jos ne a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, a nan Jihar Filato ta tsakiyar Nijeriya. Yanzu haka Ina da shekaru fiye da arba’in. Na yi karatuna na firamare a makarantar Islamiyya Pilot Science Primary School da ke cikin garin Jos. Sannan na yi karatuna na Sakandire a makarantar School for Higher Islamic Studies da ke hanyar Zariya. Na yi karatun diploma ɓangaren nazarin koyar da ilimin Larabci da Addinin Musulunci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, wato ABU Zariya. Na kuma yi karatun digirina na farko a vangaren Ilimin Sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa a Jami’ar Bayero da ke Kano, ya yi difiloma ta neman ƙwarewa wato PGDE a nan Jami’ar Jos a ɓangaren ilimin kimiyyar lafiya. Na kuma yi digirina na biyu a ɓangaren kimiyyar lafiya har yanzu.

Ba ni labarin yadda matakan da ka bi na rayuwa har ka kawo wannan matsayi da ake kai na yanzu.

To, ni dai tun tasowa ta duk wanda ya san ni ya san ni mutum ne mai ƙwazon neman na kansa, ba na son zaman banza. Tun ina ƙarami ina zuwa makaranta, ina kuma zuwa kasuwa, inda nake sana’ar ɗan kunne, na yi kuma sana’ar achava. Daga baya na buɗe wajen aikin ɓab’i wato maɗaba’a, na kuma yi aikin koyarwa a makarantu daban-daban a ɓangaren boko da Arabiyya.

Na yi aikin koyarwa a makarantun koyar da ilimin sarrafa kwamfiyuta. Daga bisani na buɗe wata makaranta ta koyar da yara ƙanana da matan aure, wacce ke ƙarƙashin kulawar Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Sannan har wa yau na buɗe makarantar koyar da aikin jinya da kiwon lafiya ta Sahlan College of Health Science Technology. Daga shekarar da aka kafa wannan makaranta zuwa yanzu ta yaye ɗalibai fi dubu, maza da mata, waɗanda yanzu haka wasun su sun samu ayyuka a wasu manyan asibitoci da cibiyoyin lafiya daban-daban a sassan ƙasar nan. Daga cikin tsarin da muke tafiya a kai akwai shirin tallafawa marayu da masu ƙaramin ƙarfi, waɗanda ba sa iya biyan kuɗin makaranta, inda muke ba su tallafin karatu. Ni kaina a yanzu haka ban san adadin marayun da yaran marasa gata da suke karatu ba tare da biyan ko kwabo ba. 

Ko za ka gaya mana sirrin samun nasarar ka, duk da ƙarancin shekarun ka, har ka kai ga cimma waɗannan nasarori masu yawa haka?

Alhamdulillahi. Ni tun tasowa ta da sauran ‘yan uwana iyayen mu sun ɗora mu a kan turbar tausayin abokan zama da ganin girman na gaba. Don haka muka taso da wannan tausayawar a zukatan mu, shi ya sa ba ma sake da duk wata dama da aka samu da za ta ba mu zarafin yin wani abu da wasu da dama za su amfana ta dalilin mu. Wannan shi ne sirrin jajircewar mu da sadaukarwar da muke nunawa wajen neman abin da jama’a za su ci moriyar sa. Duk inda na shiga ba na yarda in ci ni kaɗai, ina jawo ‘yan uwa da abokan arziƙi da ake rayuwa tare, da makwafta na unguwa, duk domin a gudu tare a tsira tare.

Mai ya zaburar da kai ka ga ya kamata ka shiga harkokin siyasa?

Wato wannan duk yana cikin burin da na daɗe da shi ne a raina na ganin na samu damar da zan taimaka wa wani ko wata al’umma da nake ganin suna cikin buƙata. Akwai wasu abubuwan da duk son ka da ka taimaka ba za ka iya ba, idan ba kana cikin gwamnati, ko kana riƙe da wasu madafun iko ba. Wannan dama ta siyasa ita ce muke ganin za ta taimaka mana mu kai ga cimma wannan buri namu. Ta siyasa ne za ka kai kukan jama’ar ka ga gwamnati, ka wakilce su a inda ba za su iya zuwa ba, ka kuma karɓo musu haƙƙoƙin su na ‘yan ƙasa da duk inda ya kamata.

Mai ya sa ka yanke shawarar tsayawa takarar neman kujerar Sanata a ƙarƙashin wannan Jam’iyya ta APC, duk da yanayin shekarunka?

Babu shakka wannan kujera za ta taimakawa jama’ar mu ta hanyoyi da dama. Sannan na lura, bisa irin wayewa da muke da ita, a wasu sassan ƙasar nan, irin yadda jama’a a wasu yankunan suke cin moriyar siyasa daga wakilansu na Majalisar Ƙasa. Amma mu a nan ba ma samun wannan gatan.

Na taɓa zuwa wani yanki a Jihar Kano, inda na ga wani ɗan Majalisar Dattijai da ke wakiltar ƙananan hukumomi goma sha ɗaya, amma yana yi musu ayyuka kamar shugaban ƙasa, amma mu a wannan shiyya ƙananan hukumomi 6 ne kacal, ba ma cin wata mo.  iya ta dimukraɗiyya, a matsayin mu na ‘yan ƙasa. Don haka muka yi tunanin ganin, in har muka samu damar shiga cikin wannan majalisa, babu shakka za mu yi abubuwa masu yawa fiye da ninki uku, wanda jama’ar mu za su ci moriyar su, kuma harkokin su na rayuwa su bunƙasa.

Na lura cewa, duk wata shaida da ake buƙata ko ƙwarewa a kan neman wannan kujera ta Sanata muna da ita, kuma muna da kyakkyawan fatan za mu yi fiye da abin da waxancan suke yi, domin mun ga kamun ludayin waɗanda suka riƙe kujerar na baya da abin da suka yi, wanda bai amfanar da al’ummar wannan yanki da komai ba. Muna buƙatar kyakkyawan jagoranci, gaskiya da tafiya tare da kowanne ɓangare, don samun bunƙasar rayuwar al’ummar mu, da haɗin kan mu baki ɗaya.

Yankin da ka fito kuma ka ke takarar zama wakilinsa a Majalisar Ƙasa, yanki ne da ya sha fama da rikice-rikicen addini da ƙabilanci, yaya ka ke ganin za ka taimaka wajen shawo kan waɗannan matsalolin, idan ka samu damar shiga Majalisa?

Zaman lafiya abu ne mai matuƙar muhimmanci ga kowacce al’umma, musamman ma a shiyyar Arewacin Filato, wanda rikice-rikice suka ɗaiɗaita. Don haka muna da kyakkyawan tunanin yadda za mu yi ƙoƙarin samar da fahimtar juna a tsakanin mabambantan ƙabilun da ke wannan shiyya, ta yadda kowa zai amfana da ribar dimukraɗiyya, kuma zai yaba da yadda ake tafiyar da al’amura tare da shi. Za mu shiga majalisa da ƙudirin samar da muhimman abubuwan more rayuwa ga jama’ar mu, samar da tallafin sana’o’i ga mata da wata san mu, wanda ayyuka ne da muka saba yi dama. Za mu yi ƙoƙari mu ga mun ba da dukkan tallafi da goyon bayan da ya kamata don ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro, ‘yan banga masu ayyukan sa kai, da Hukumar Samar Zaman Lafiya ta Jihar Filato saboda ƙoƙarin da suke yi wajen bunƙasa fahimtar juna da zaman lafiya.

Waɗanne ƙudirori ne ka sa a gaba cikin yaƙin neman zaɓenka, a wannan yanki?

Babu shakka akwai manufofi da dama da muka tsara mayar da hankali a kansu, da suka haɗa da samar da tallafi da kulawa ga sha’anin tsaro, za mu nemi goyon baya da haɗin kan rundunar ‘yan sanda, don samar da ƙarin ofisoshin ‘yan sanda da jami’an su, yayin da mu kuma za mu samar da tallafin kayan aiki da ake buƙata. Za mu yi ƙoƙarin jawo hankalin hukumomi da kamfanonin yin taki da za a tallafawa ayyukan gona da samar da sabbin dabarun zamani na killace kayan amfanin gona don kaucewa lalacewar kayan amfanin da ake samu. Batun bunƙasa cigaban harkokin ilimi dama a cikin sa muke, za mu yi ƙoƙarin gyaran makarantun da suka lalace da tallafawa ma’aikatar ilimi don ƙara mara wa gwamnati baya a samu inganta harkokin ilimi. Duk wani ɓangare na cigaban al’umma da ke buƙatar gyara da kulawa, a ɓangaren doka ko tallafi duk za mu yi abin da ya kamata.

Kana wannan takara ne da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa da suka fito a ƙarƙashin manyan jam’iyyu, wanne shiri ka ke da shi na fuskantar waɗannan ‘yan takara, ganin cewa ka fito ne a ƙarƙashin baƙuwar jam’iyya a Filato ta NNPP?

Kafin na shiga wannan takara sai da na yi nazari sosai na duba sahihancin jam’iyyun da ake da su, da kuma  ‘yan takarar da ake da su a waɗancan jam’iyyun da ake ganin manya ne. Na gamsu da manufofi da ingancin ‘yan siyasar da ake da su a NNPP tun daga matakin qasa zuwa jiha. Babu ma kamar shi jagoran jam’iyyar na qasa, wato jagoran mu, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon Sanata, tsohon Gwamna, kuma tsohon minista. Ba mutum ne baƙo ba a siyasar ƙasar nan. Ba ka buƙatar yi masa doguwar gabatarwa ga jama’a, don irin ɗimbin ayyukan raya ƙasa da gina al’umma da ya yi. Ba a Jihar Kano kaɗai ba, inda ta yi gwamna har karo biyu. Don haka muna son mu kwaikwayi irin halayensa, da ayyukansa na siyasa, don mu ma mu amfanar da al’ummar mu, da irin gogewar da muka samu, da kuma biyayyar da muke yi masa.

Batun abokan takara ta na sauran jam’iyyun kuwa, ba ni da fargabar kowa a cikin su. Don ba su da mutane masu daraja da nagartar da muke da su a NNPP, kuma duk inda muka je jama’a na bayyana masa farin cikin su da shigar mu wannan takara da alƙawarin mara mana baya. Saboda ba su ji daɗi a hannun ‘yan waɗancan jam’iyyun da suka zauna a wannan kujera ba. Shi ya sa suke da kyakkyawan fata a kan mu, mu kuma da yardar Allah ba za mu ba su kunya ba.

Wanne abin tinqaho ka ke da shi  na cewa kana da abin da sauran ýan takara a wannan yanki ba su da shi?

To, ai ni duk abubuwana a bayyane suke. Duk inda ka za ga cikin garin Jos, wanda shi ne babban gari da ya haɗe kusan dukkan al’ummar da ke wannan shiyyar, ba za ka kasa samun wani labari a kaina ba, ko ayyukan da nake yi na cigaban al’umma ba. Na san ba za ka kasa sanin ƙoƙarin da nake yi a ɓangaren inganta ilimin lafiya ba. Makarantar Sahlan ta yi fice wajen horar da matasa kan harkokin kiwon lafiya da tsaftar muhalli. Kuma abu mafi burgewa shi ne mun samar wa al’umma damar da yaransu za su samu ilimin da suke buƙata mai inganci ba tare da sun bar jihar ba, lura da irin ƙarancin makarantun koyar da aikin jinya da ake da su a nan Filato. Kuma tana gogayya da kowacce makaranta irin ta ba a Jihar Filato kaɗai har dukkan jihohin qasar nan. Sannan mutane da dama sun amfana da tallafin da muke bayarwa na ɗaukar nauyin jarabawar kammala sakandire, koyar da sana’o’in dogaro da kai, da ɗaukar nauyin yi wa mata masu juna biyu awon ciki kyauta, wanda ko gwamnatin Jihar Filato ba ta ba da irin wannan tallafi. Haka kuma a ɓangaren Kula da walwalar jama’a muna ba da gudunmawa a cikin anguwanni da ƙauyuka, game da abubuwan da suka shafi tsaro, gyaran hanya, samar da ruwan sha da sauran su. Duk waɗannan abubuwa ne da muka yi, a matsayin mu na ɗaiɗaiku masu kishin cigaban al’umma, ba jami’an gwamnati ko masu riqe da muƙaman siyasa ba. Kuma muna kan yi ba mu tsaya ba. Saɓanin su sauran abokan takara ta da za suka riƙe muqamai daban-daban, kuma suka samu damar da tafi wanda muke da shi, amma ba su iya tunawa sun yi wa al’umma rabin abin da muke yi ba.

Wanne abin koyi ka ke ɗauka daga Madugun Jam’iyyar NNPP, kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso?

Sanata Rabi’u Kwankwaso tsayayyen mutum ne mai gaskiya da gogewa a kan harkokin siyasa. Salon yadda yake tafiyar da siyasar sa yana burge ni sosai. Wannan shi ne abin da muke koyi daga wajen sa. Da ikon Allah duk wani abu da ba gaskiya ba, ko wanda muka san ba hurumin mu ba ne, za su gaya wa mutane ba mai yiwuwa ba ne, wanda za mu iya kuma za mu ba da dukkan ƙarfin mu, don mu ga cewa jama’a sun amfana. Sannan yadda yake yake nuna damuwa da matsalolin talakawa da cigaban rayuwar ‘ya’yansu. Abubuwan da Kwankwaso yake yi na inganta rayuwar talakawa da samar da tsare-tsare na cigabansu, kamar yadda ya bayyana a manufofinsa na takarar shugaban qasa da yake yi, a wannan jam’iyya tamu mai albarka.

Mene ne babban burin ka a yanzu?

Babban burina bai wuce in ga rayuwata tana amfanar da al’umma ba. Da Duk wani abu da Allah ya hore mana, kama daga arziƙi, lafiya, ilimi da duk wani ci gaban rayuwa da rayuwar wani za ta inganta.

Mene ne kiranka ga al’ummar mazaɓar kujerar Sanata a shiyyar Filato ta Arewa?

Kirana gare su su tashi su ba da gudunmawa don kawo canji ga rayuwar su da wannan mazaɓa ta mu, ta yadda za su zavi shugabanni nagari da za su wakilce su a Majalisar Ƙasa. Ina fatan za su bani dama a ranar zaɓe, don ganin mun yi abin da ya dace, na kawo wa yankin mu cigaba. Abu mai muhimmanci na ƙarshe shi ne su tabbatar sun yi zave, kar mu zauna a gida mu yi tunanin za mu ga canji a rayuwar mu da ƙasar mu.

Na gode.

Ni ne da godiya.