An kai wa jarumi Akeem Adeyemi hari a wurin ɗaukar fim

Daga AISHA ASAS

Fitacciyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kudu Wumi Toriola, ta bayyana labarin tsautsayin da ya afkawa abokin aikinta Akeem Adeyemi, a wani faifan bidiyo da ta fitar a shafinta na Istagram, wanda ke ɗauke da labarin yadda abin ya faru cikin murya da hotuna.

An hasko jarumi Akeem, yana darzar kuka a faifan bidiyon, bayan da wasu tsageru suka kai masa hari a lokeshon, inda ya je da zumar ɗaukar wani shirin fim.

Kamar yadda jarumar ta bayyana a a ƙarƙashin bidiyon, tsagerun sun hargitsa wurin ta hanyar mayar da muhallin mai cike da kwanciyar hankali da natsuwa ta masu shirin fara harkar fim zuwa wurin hatsaniya da zubar jini.

“ku kalli yadda tsageru suka aikata, wurin gudanar da shirin fim ne ya koma haka.” Inji jarumar.

Hakazalika ƙwararren jarumi Adebayo Salami, shi ma ya tofa lbarkacin bakinsa, inda ya tabbar da yanzu haka waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki an cabke su, suna hannun hukuma.

Baya ga haka, Adebayo ya yi kira ga ƙungiyar TAMPAN, wato Theatre Arts and Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria da ta ɗau babban mataki, don ba wa mambobinta kariyar da ta dace.

“Wannan aika-aikar ba abin kawar da ido ba ce, kuma ba za mu lamunta ba, duk da cewa, na yi matuƙar murna da cewa, hukuma ta damƙe waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin, sai dai Ina mai kira ga Theatre Arts and Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria, da ta kali wannan lamari tare da yin abinda ya dace cikin gaggawa.” A cewar sa.

Jarumi Salami ya ƙara da cewa, “kariya ga lafiyar masu shirya finafinai ce babban abu mai muhimmanci a wurin mu. Kuma idan aka yi duba da hasaran da irin wannan lamari ke janyowa, za ka tarar ba ƙaramin ci-baya ba ne ga masana’antar tamu, domin ko baya ga cin zarafi da aka yi ga jarumin, rasa rana ɗaya ga aikin fim na nufin ƙarin kuɗin da za a kashe daga kuɗin da aka kasafa a aikin.

“Ba wani mai shirya fim da zai so ya shiga wannan hali. Ina mai miƙa jaje na gpa jarumi Akeem Adeyemi da sauran waɗanda abin ya shafa.”