Buhari ya kinkimo bashin tiriliyan N3 duk da tiriliyan N45 da ake bin gwamnatinsa

Spread the love

Gwamnatin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Buhari ta sake kinkimo bashin Dalar Amurka biliyan $9 daidai da Naira tiriliyan 3.98 daga Bankin Duniya.

Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Shubham Chaudhuri ne ya bayyana haka a wajen taron da ya shirya a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata.

Shubham Chaudhuri ya ce, zaman Bankin Duniya a Nijeriya ba shi da burin da ya wuci taimaka wa ƙasar ficewa daga ƙangin talaucin da take ciki da kuma inganta rayuwar al’ummarta.

A baya, jaridar Intel Region ta rawaito cewar, bashin da ake bin Nijeriya ya ƙaru zuwa Naira tiriliyan N45.8 ($103 billion) a gaɓar farko ta 2022.

A cewar Bankin Duniyar, a cikin watanni 30 da suka gabata ya samar wa Nijeriya kuɗi sama da Dala biliyan 9 da ruwa mai sauƙi.

Ya ƙara da cewa, waɗannan kuɗaɗe ba tallafi ba ne; bashi ne mai rangwame sosai.

haka nan, ya ce ya kamata a kalle su a matsayin amintattun abokan tarayya, kuma “Duk abin da za mu iya yi don taimakawa Nijeriya, za mu yi,” in ji Bankin.

By Editor