Batun raba katin zaɓe

Assalam alaikum. Fara ba da katunan zaɓe na dindindin ga wasu daga cikin masu zaɓe a Nijeriya ya ja hankalin ‘yan ƙasa inda kowa ke bayyana ko tofa albarkacin bakinsa.

A wannan Litinin din Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Inec ta soma wannan aiki kuma mutanen da za a bai wa katunan su ne mutanen da suka ba da sunayensu daga farkon 2022, zuwa lokacin da aka rufe aikin a watan Yuli.

Sai dai kuma duk da irin tsare-tsare da INEC ta ce ta yi, ana ta samun masu ƙorafi da kokawa kan dogayen layuka wajen samun katin, da kuma waɗanda suka hau shafukan sada zumunta musamman Tuwita da nasu ƙorafin.

Za dai a shafe kwanaki ana wannan aiki na raba katunan zave a matakin ƙaramar hukuma kafin a koma matakin mazaɓu.

Ana raba katunan ne a ofisoshin INEC na ƙananan hukumomi kawo yanzu, inda jama’a ke bin layi a mazaɓu.

Duk mutumin da ya zo karɓar katin sai ya gabatar da shaidar cewa ya yi rijista a baya sannan sai a duba sunansa a kundin rijistar zaɓe sai kuma a duba masa katin.

Idan an sami katin sai kuma a rubuta sunansa ya saka hannu cewa ya karɓar.

Amma da farko sai mutum ya duba sunansa a kundin rijistar da aka yi baje-kolinta a jikin bango.

Waɗanda ba su ga sunayensu ba a kan ba su wata takarda su cike sannan sai a buƙaci su dawo daga baya don karɓar katinsu.

Sai dai wasu rahotanni na cewa ana samun dogayen layuka wajen karɓar kati, sannan akwai waɗanda ba su samu katinsu ba saboda wasu dalilai.

Wasiƙa daga AHMAD MUSA, 07041094323.