Gudaji da fadar Aso Rock: A gano mana gaskiya!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tun 2003 da Shugaba Buhari ya fara neman takarar shugabancin Nijeriya ya ambata batun yaƙi da cin hanci da rashawa ya zama cikin kan gaba a abubuwan da zai yaka matuƙar Allah ya ba shi nasarar lashe zaɓe. Hatta a jawabin kifar da gwamnatin farar hula ta shugaba Shehu Shagari a jamhuriyya ta biyu, shugaba Buhari ya kawo dalilan amshe madafun ikon da yadda ’yan siyasa suka afka cin hanci da rashawa.

A wannan lokacin ta kai ga shugaban amincewa da ɗaure mutane fiye da shekaru 100 a gidan yari don samun su da laifin zarmiya. Ga wanda Allah ya sa zai tuno labarin tsohon ministan sufuri maraigayi Umaru Dikko, zargin ya azurta kan sa da dukiyar gwamnati ya sa yunƙurin ɗauko shi a cikin akwati daga London amma hakan bai yi nasara ba don gano jami’an da su ka tafi aikin a filin jirgin sama. Umaru Dikko ya tsallake rijiya da baya kuma daga bisani ya shiga ƙalubalantar gwamnatin ta hannun gwamnatin Burtaniya da cewa ta fito da shaida ta nuna haƙiƙa ya zambaci Nijeriya ko ya wawure dukiyar baitul malin Nijeriya.

Dikko wanda har ya rasu bai yi musabaha da shugaba Buhari ba ya ce Buhari bai fahimce shi ba don mutane irin sa mulki ne kawai a gaban su na muƙamin a ke gani amma ba burin su tara dukiya ba. Labarun da mu ka samu ta bakin ɗan siyasa a lokacin Abdulkarin Daiyabu wanda ya zama shugabantar wata ƙungiyar mai taken “RUNDUNAR ADALCI” sun nuna a jamhuriya ta biyu mutum uku ne kacal ba a samu da laifin almundahana ba da su ka haɗa da shi marigayi shugaba Shehu Shagarin kansa, marigayi Alhaji Adamu Ciroma da Bilyaminu Usman ƙaramin minister Dan Hadeja. In haka ne bayan shekaru 30 da shugaba Buhari ya dawo mulki ya dace ya yi bitar irin waɗancan matakan a tsari irin na dimokraɗiyya wajen hukunta waɗanda a ka samu da laifin durƙusar da tattalin arziki ta hanyar rashin riƙon amana a ofisoshin gwamnati.

Shin yaƙi da cin hanci da shugaba Buhari ya fi ambatawa hatta lokacin da ya kwave rigar soja ya zama cikekken farar hula ya cimma burin ɗaukar takobin yaƙin ya ci gari ko dai akwai matsaloli da a ka riƙa samu a fagen dagar? Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da ya rasa kujerarsa a ƙarshen nan wato Ibrahim Magu ya sha ambatawa cewa in ka na yaƙi da cin hanci to shi ma hancin sai ya yake ka. Irin zargin da a ka yi ma sa duk da ba kotu ce ta zauna don duba batutuwan ba wani kwamitin ne da ma zuwa yanzu bai fitar da rahoton sa dalla-dalla ba, za mu ce abun tsoro ne ainun.

Lalle kuwa dole Magu ya ciji yatsa ya yi takaici ga zargin da a ka yi ma sa na cewa ya kan sace kayan satar da ya ke kwatowa. In kuwa mai yaƙi da sata zai zama babban mai sata ai ba ribar kwato dukiyar ma tun da ba za ta koma aljihun gwamnati ba. Na tabbata yawancin ‘yan Nijeriya masu tunani irin na wa za su so jin gaskiyar abun da ya faru a lokacin jagorancin da Magu ya yi a hukumar yaƙi da cin hanci EFCC.

In kuma batun ya mutu an naɗa sabon shugaba a hukumar mai jajircewa wajen yaain shikenan sai kowa ya maida wuƙa kube. Duk wannan shunfuda ce ta darasin wannan makwan kan wani zargi da ya yi tambari tun ƙarshen makwan jiya da ɗan majalisar wakilai Muhammad Gudaji Kazaure ya yi na wasu biliyoyin kuɗi da ba sa amfanar gwamnati.

Wani kwamitin bincike na mutum 7 da shugaba Buhari ya kafa a asirce don duba ayyukan tara kuɗaɗen shiga na yau da kullum na bankuna, ya gano zunzurutun kuɗi da su ka kai dala biliyan 171 da babban bankin Nijeriya ya ajiye a wani asusun da ba ya amfanar gwamnati. Kwamitin ya ce kuɗin za su iya taimakon Nijeriya ta rage jibgin bashin da a ke binta.

A takarda da aka nunawa manema labaru ta nuna membobin kwamitin mai mutum 7 sun haɗa har da shugaban rundunar tsaron farin kaya DSS, ministan shari’a Abubakar Malami, ministar kuɗi Zainab Shamsuna da tsohon kwamishinan ’yan sanda na Kano Muhammad Wakili.

Sakataren kwamitin ɗan majalisar wakilai Muhammad Gudaji Kazaure ya bayyana cewa, sun yi tsayin daka har sai da gwamnan baban banki Godwin Emefiele ya bayyana gaban kwamitin inda a ka ba da belinsa amma bincike na cigaba da gudana.

Gudaji Kazaure ya ce, su na da cikekken goyon bayan shugaban ƙasa amma zuwa yanzu shi kan sa ya ƙasa ganin shugaban don bayyana ma sa halin da a ke ciki.

Kazaure ya ce, sauya fasalin kuɗin a da nasaba da shashantar da binciken da su ke gudanarwa. Gwamnan babban banki Emefiele ya bayyana cewa na sa dalilan sauya fasalin kuɗin ne bayan gano maƙudan kuɗin da ya dace su zauna a bankuna su na ɓoye a hannun jama’a.

Emefiele ya ce, fiye da Naira tirilyan 2.7 cikin Naira tirilyan 3.2 na hannun jama’a ne da wasu su ka ɓoye kuɗin. Emefiele ya ce fiye da kashi 85% na kuɗin da a ka buga na hannun jama’a da ke voye kuɗin. Hakanan sauya kuɗin zai taimaka wajen yaƙi da ɓarayin daji da kan jibge kuɗi a daji ta hanyar lalle su dawo kuɗin don komai ya riƙa bi ta cikin banki.

Bayan nan ma babban bankin ya ɓullo da takaita fitar da kuɗi a wuni zuwa Naira dubu 20 ga ɗaiɗaiku inda kamfanoni ka iya fitar da Naira 100 wato a mako mutum shi kaɗai ka iya fitar da Naira dubu 100 inda kamfanoni za su riƙa fitar da dubu 500. Tsarin a cewar babban bankin zai dawo da amfani da na’ura wajen hada-hadar kuɗi maimakon yadda mutane ki jidar kuɗi sun a yawo da su.

Masu marawa tsarin baya ma na cewa dabara ce da za ta hana ’yan siyasa masu son murɗe zaɓe ta hanyar amfani da toshiyar baki wajen samun wadatattun kuɗin da za su iya yin hakan. Shugaba Buhari dai ya nuna gamsuwa ga sauya fasalin kuɗin don ma shi da kan sa ya ƙaddamar da sabbin kuɗin da abun da a ka lura shi ne an sauya kala ne ta hanyar misali ɗora kalar Naira 500 kan Naira 200 hakanan Naira 200 kan Naira 500 inda Naira dubu ma ta sha sabon fenti.

Za a jira a ga yadda kwamitin zai yi bayan duba belin da ya ba wa gwamnan da kuma fatar ganawa da shugaba Buhari

Muhawara ba ta ƙare ba don har yanzu ana musayar bayanai kan rahoton da ɗan majalisa Gudaji Kazaure ya fitar cewa a na karkatar da biliyoyin dala da babban banki ya tara daga kuɗaɗen da bankuna ke caji daga shigarwa ko cire kuɗi.

Kazaure ya ce, kuɗin a Naira sun kai Naira tirilyan 89.9 da a kan tura su ga masu zuba jari ta zamba cikin aminci alhali kuɗin na gwamnati ne.

Kazaure wanda ya ce, duk ƙoƙarin da ya yi na ganawa da shugaba Buhari da ya ce ya naɗa shi sakataren kwamitin bincike ya ci tura, amma gwamnan babban banki da su ke zargi na zaman beli ne.

Mai taimakawa shugaba Buhari kan labaru Garba Shehu ya fitar da sanarwa da ke cewa ministan shari’a Abubakar Malami ne ke gudanar da aikin kwamitin a halin yanzu bayan rushe wanda Kazaure ke magana.

Shehu ya ƙara da cewa, shugaba Buhari na kaunar aikin kwamitin da Malami ke jagorantar kuma kwamitin na gudanar da aikinsa don dawo da kuɗaɗen cajin zuwa asusun tara kuɗaɗen na bai ɗaya.

Kazaure ya ƙalubalanci Garba Shehu da cewa tamkar ya na baiyana ra’ayinsa ne don bai ma san lokacin da a ka kafa kwamitin ba.

Majalisar Dattawan Nojeriya ta buƙaci babban bankin Nijeriya CBN ya sake tunani kan takaita fidda kuɗi a na’urar ATM da ma bankuna da a ke shirin faraway aiwatarwa daga 9 ga watan gobe.

Majalisar ta tafka muhawara inda akasarin masu bayanai su ka yi rinjayen CBN ta sake bitar batun don zai iya zama matsala ga jama’a.

Hatta Sanata Yusuf A Yusuf da ke mara baya 100% ga shirin da nuna zai ma taimakawa darajar Naira da tsaro, ya samu rashin amincewa daga Sanata Adamu Bulkachuwa da ke cewa sam ba wani tsaron da shirin zai kawo.

Sanata Adamu Aliero ma ya buƙaci sake duba matakin don akwai al’ummar karkara da ba sa ma amfani da bankuna.

Orji Kalu ya ba da shawarar a sauya tsarin zuwa Naira dubu 500 ga daidaiku sai kuma Naira miliyan 3 ga kamfanoni ko cibiyoyi.

Kammalawa;

Haƙiƙa wannan gwamnati dai ta shugaba Buhari na daga gwamnatocin da su ka zo da farin jini sosai bayan doguwar gwagwarmayar da talakawa su ka yi. Waɗanda su ka yi gwagwarmayar nan don fatar samun ingancin rayuwa ne inda da dama su ka rasa ran su wasu kuma su ka rasa dukiya. A sauran watannin da su ka ragewa gwamnatin ya na da kyau ta fito ta yi bayanan duk abubuwan da a ka yi tsammanin za ta iya yi amma a ka samu ƙalubale ba su samu ba.