Badaƙalar kuɗin harajin bankuna

A Nijeriya, batun harajin da bankuna ke cire wa waɗanda suka yi amfani da asusun ajiya wajen tura kuɗi ko cirewa na cigaba da janyo cece-kuce.

A makon da ya wuce ne kwamati na musamman da Shugaba Muhammdu Buhari ya kafa domin gudunar da bincike kan cajin cirewa da ajiyar kuɗi a asusun banki ya yi zargin cewa wasu hukumomin da binciken ya shafa suna ƙoƙarin hana shi yin aikinsa, da kuma hana shi ya mika wa Buhari rahotonsa.

Sai dai sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mai magana da ywun shugaban Nijeriya Malam Garba Shehu ya ce lokacin da Shugaba Buhari ya karbi ragamar ƙasar a shekarar 2015 ya samu wannan doka ta cajin kuɗin haraji da bankuna ke karɓar idan an tura kuɗi, amma kuma ba a aiki da ita yadda ya kamata ba.

“Lamarin ya kara taɓarɓarewa, bayan da aka smu wasu da suka haɗa kai da hukumar saƙon gidan waya wato NIPOST, inda aka yi zargin an adana kuɗin cikin aljihunsu bayan wata hukumar gwamnati ta zuba zunzurutun kuɗi har naira tiriliyan 20 tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016, tare da ikirarin za a iya gano kuɗin tare da zuba su a lalitar gwamnati,” a cewar sanarwar.

“Kwararrun da za su nemo kuɗaɗen sun buƙaci a ba su kashi 7.5 cikin 100 na kuɗaɗen ƙarƙashin sa idon tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugabn Ƙasa Marigayi Malam Abba Kyari, kamar yadda ya rubuta wasiƙa a watan Maris na 2018 kan ƙorafin rashin yin abin da ya dace daga waɗanda aka ɗora wa alhakin bincike kan batun.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa Abba Kyari ya kuma buƙaci a dakatar da kwamatin ƙwararrun masu ba da shawarar lalubo bakin zaren, inda aka karkatar da kuɗaɗen. Kan haka ne su kuma suka kai ƙarar gwamnatin Nijeriya.

Batun har gaban kuliya ya je kuma bayan tsawon lokaci ana tattaunawa a kotun, gwamnatin Nijeriya ta yi nasara.

Bayan haka ne kuma aka sake mayar da batun gaban majalisar dokoki, tare da yi wa dokar kwaskwarima da kuma cire NIPOST daga karɓar harajin.

“Wannan dalili na rasa samun kuɗaɗen da kwamitin ya yi, shi ne suka fara ta da jijiyar wuya da ɗaukar sabon salon yi wa gwamnatin Nijeriya barazana a fakaice,” inji gwamnatin Nijeriya.

Garba Shehu ya ce, “A baya-bayan nan sun sake dawowa, suka yi amfani da Honrabul Gudaji Kazaure da aniyar wai za su sake bibiyar batun kuɗin harajin da bankuna ke cire wa abokan hulɗa da kamfanoni, sun kuma naɗa wani shugaban kwamati yayin da shi kuma Kazaure yake sakatare.

“Bayan dawowar shugaban kwamitin da Marigayi Abba Kyari ya rusa a wasiƙar da ya aike wa shugaban ƙasa a watan Maris na 2018, a matsayin shugaban sabon kwamitin, Shugaba Buhari ya janye amincewar da ya bai wa kwamatin na aikin tun farko.”

Gwamantin Nijeriya ta damu kan sanya sunan Alƙalin Alaƙalai Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin mamban kwamatin, da kuma ɗan majalisa mai ci a matsayin sakatare, wanda a cewarta hakan ya sava wa sashe na 5 (1),(a) da (b) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999 (da aka yi wa kwaskwarima).

“Kwamatin ya rasa damar yin aiki tun daga lokacin da Shugaba Buhari ya dakatar da shi. A dan tsakanin nan, ana ta ce-ce-ku-ce da muhawara kan ko kwamitin na da sahihanci ko a’a, ko ya ci gaba da aiki ko a’a.

“Mutane na da damar faɗin abin da suke so, hakan ba zai sauya matsayar kundin tsarin mulkin Nijeriya ba, kuma shugaban ƙasa na da ƙarfin ikon naɗawa da sauke wasu a ƙungiyance kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi iko.”

Garba Shehu ya ce, ya yi mamakin yadda ɗan kwamitin kuma mamba a jam’iyyarsu, Honabul Gudaji Kazaure ya nemi tsoma shi cikin danbarwar.

“A bayyane take ƙarara kwamitin da ke ikirarin kuɗin da ya kai naira tiriliyan 89 na kuɗin harajin da ake cirewa ‘yan ƙasa ba gaskiya ba ne, lissafin dokin rano ne,” inji shi.

A shekarar 2016 ne kwamitin ya ce an karɓi naira tiriliyan 20 amma baki ɗaya kuɗin da bankin ya sanya bai kai rabin tiriliyan 89, ya kuma so yin shiru amma sai ya ga Honarabul Gudaji na son janyo shi cikin batun.

“Batun ba shi da tushe ballantana makama, kuma kuɗaɗen da ake magana a kai sun yi yawan da hankali ba zai ɗauka ba, sannan shi kansa Babban Bankin Nijeriyar [CBN] ba shi da irin kuɗaɗen.”

Wasiƙa daga MUHAMMAD AUWAL, 08062327373.