Sin ta gudanar da taron shekara-shekara na ayyukan tattalin arziki don tsara shirin shekarar 2023

Daga CMG HAUSA

Daga ranar Alhamis zuwa Juma’a 16 ga wata ne, aka gudanar da babban taron kolin tattalin arziki na shekara-shekara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda shugabannin kasar Sin suka yanke shawarar kan sassan da za a ba da fifiko kan ayyukan raya tattalin arziki na shekarar 2023.

Da yake gabatar da muhimmin jawabi a yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi nazari kan ayyukan tattalin arzikin kasar a shekarar 2022, tare da nazari kan halin da ake ciki a fannin tattalin arziki, da kuma tsara aikin raya tattalin arziki na shekarar 2023 dake tafe.

A yayin taron, an bayyana cewa, ana sa ran samun farfadowa da ingantuwa baki daya ta fuskar tattalin arzikin kasar a shekara mai zuwa, kuma ya zama tilas a tabbatar da kwarin gwiwar yin aiki mai kyau a fannin aikin raya tattalin arziki.

Taron ya bukaci samun daidaito a fannin tattalin arziki a matsayin abu mai muhimmanci, tare da neman ci gaba mai dorewa, da tabbatar da daidaiton tattalin arziki a shekara mai zuwa.

A cewar taron, za a ci gaba da aiwatar da manufofin kasafin kudi mai dorewa da sanya ido yadda ya kamata a shekara mai zuwa. A halin da ake ciki kuma, za a yi kokarin karfafa ikon sarrafawa da daidaita manufofi daban-daban, domin samun ci gaba mai inganci.

Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa