Barazanar jefa ƙuri’ar ƙananan yara

Ƙuri’ar ’yan ƙasa da shekaru 18 wata ɓarna ce a tsarin zaɓen Nijeriya. Shekarun da suka cancanci shiga zaɓe a ƙasar sune ’yan shekaru 18 zuwa sama. Sai dai a lokacin zaɓe, ana barin yara su kaɗa ƙuri’a a wasu sassan ƙasar. Wani lokaci ma matattu ma suna yin zaɓe. Kuma wannan shine tushen fara rigingimu. Lokacin da aka ba wa yaran da ba su kai shekarun jefa quri’a damar jefa ƙuri’a ba, hakan yana kawo cikas ga sahihancin tsarin zaɓe kuma yana sanya alamar tambaya kan sakamakon aikin.

A kwanakin baya, gamayyar ƙungiyoyin farar hula 10 (CSO) sun koka kan yadda aka gano masu kaɗa ƙuri’a masu ƙarancin shekaru 84,000 a jihar Filato. Ƙungiyar ta gano cewa rajistar masu kaɗa ƙuri’a ta cika da ƙananan yara da suka haɗa da ’yan ƙasa da shekaru biyar. Haka kuma ana zargin an yi rajista da yawa a ƙananan hukumomi biyar cikin 17 na jihar. Ƙungiyoyin CSO sun buƙaci Hukumar Zaɓe Mai ziaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gaggauta tsaftace rijistar masu zaɓe a jihar Filato da ma faɗin ƙasar baki ɗaya. Mun lura da cewa ba a jihar Filato kaɗai ake yin hakan ba, har ma da sauran jihohin tarayyar ƙasar nan, musamman a Arewa.

Jihar Kano dai ta yi ƙaurin suna wajen wannan matsalar. Misali, a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ƙananan hukumomi 44 na jihar a watan Janairun 2021, an yi ta yaɗa zarge-zargen zaɓen ƙananan yara. Kafofin yaɗa labarai da masu sa ido kan zaɓen sun lura cewa yara ‘yan ƙasa da shekaru tara ne suka shiga zaɓen suka cika ta. An yaɗa hotuna da faifan bidiyo na zaɓen ƙananan yara a shafukan sada zumunta wanda hakan ya ɓata wa wa mutane da dama rai. Wannan bai dace ba domin kuwa saɓa wa Kundin Tsarin Mulki ne da kuma Dokar Zaɓe. Wani nau’i ne na maguɗi.

Zaɓen ƙananan yara na faruwa ne saboda ƙwarin gwiwar ‘yan siyasa na samun nasara ko ta halin ƙaƙa. Galibi, jam’iyya mai mulki ta kan yi wannan aiki ne domin ta samu ƙuri’u masu yawa a inda ba a sonta ko kuma inda suka fatattaki masu kaɗa ƙuri’a da ’yan daba ko jami’an tsaro. Suna amfani da yara don jefa ƙuri’a don bayyana cewa an sami fitowar jama’a da yawa kuma don tabbatar da cewa sun samu duk wani adadi na ƙuri’a

Baya ga yin amfani da yara masu jefa ƙuri’a, ‘yan siyasa kuma suna yin wasu abubuwan da ba su dace ba don cin gajiyar abokan hamayyarsu. A ’yan kwanakin nan, alal misali, an ɗauki nauyin wasu ’an daba don kona ofisoshin INEC a sassan ƙasar nan. Fiye da 50 daga cikin irin waɗannan hare-haren an rubuta su a faɗin ƙasar. Ya faru ne a wurare kamar Ebonyi, Imo, Anambra, Enugu, Ogun da Osun. Wannan ya haifar da lalata muhimman kayayyaki kamar akwatunan zace, rumbun jefa ƙuri’a, samar da saiti da Katunan Zaɓe na Dindindin (PVC) da waɗanda ba a tattara ba.

Duk waɗannan sun kawo babban ƙalubale ga babban zacen 2023. Idan ba a yi maganinsu ba, za su iya ɓata sakamakon zaven. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, ya kamata ace ta gano masu kaɗa ƙuri’a masu qarancin shekaru tare da hana su kaɗa ƙuri’a. A bayyane yake cewa yara ba su fahimci abubuwan da ke tattare da jefa ƙuri’a ba. Abin baƙin ciki ne yadda jami’an jam’iyya da ma jami’an tsaro suka tsunduma cikin wannan aika-aika. Don haka ya kamata INEC da jami’an tsaro su ƙara zage damtse wajen kamawa tare da hukunta waɗanda ke da hannu a wannan haramtacciyar harƙalla.

Muna jinjina wa shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu na cewa hukumar za ta gudanar da sahihin zaɓe ga ’yan Nijeriya a 2023. Ya bayyana cewa hukumar ta ƙudiri aniyar ganin zaɓen 2023 ya zama mafi kyawu da aka taca samu a Nijeriya. Domin kuwa duk abubuwan dimokuraɗiyya za a aiwatar. A wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels kwanan nan, Daraktan wayar da kan jama’a masu kaɗa ƙuri’a na INEC, Victor Aluko, ya kuma ba da tabbacin cewa za a tsaftace rajistar gaba ɗaya, kuma babu wani mai ƙarancin shekaru da zai kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2023.

INEC na buƙatar ƙara yin aiki. Tana buƙatar a ƙara taka-tsantsan. Muna kira ga alƙalan zace da su hanzarta aiwatar da sabunta rijistar masu zaɓe, domin kawar da abubuwan zamba masu neman wurin zama. Bayan da ya tabbatar mana da cewa ba za su yarda da masu kaɗa ƙuri’a masu ƙarancin shekaru ba, kuma za su tsaftace rajista, ya kamata INEC ta cire sunayen ƙage daga cikin rajistar.

Wajibi ne hukumomin tsaro da abin ya shafa su kasance cikin shiri. Yawancin lokuta, suna kallon wata hanya yayin da ake shigar da yara masu jefa ƙuri’a ta wata hanyar. Dole a bar waɗanda suka mallaki hankalin kansu su kaɗa ƙuri’a.

Wajibi ne INEC ta haɗa kai da CSO da jami’an tsaro domin kamo masu laifin. Kamata ya yi ta kama tare da hukunta duk waɗanda ke da hannu wajen tallafawa zaɓen ƙananan yara a ƙasar nan. Ya kamata kuma ta sanya takunkumi ga ma’aikatanta da ke ba da damar kaɗa ƙuri’ar a yankunansu. Ya kamata ’yan Nijeriya su tabbatar da cewa akwai tsarin wauta a zaɓen da ke tafe.