Yadda birrai suka sha bidiri a tsakiyar gari a Thailand

Spread the love

Birrai a birnin Lopburi na ƙasar Thailand sun sha lagwada tare da dabdala a wajen bikin Dabdala ta Birrai ta Shekara da ake shiryawa a tsakiyar Thailand.

Kafar labarai ta AP, ta ce, a daidai lokacin da ake fama da cinkoson safiya, sai mutanen da suka yi shigar batum-batumi a matsayin birrai suka jejjeru a wajen wani tsohon ginin tarihi da ake kira Ancient Three Pagodas, yayin da ’yan sa-kai suka tsara abinci a gefen hanya domin birrai na gaskiya — a matsayin wani biki na yankin Lopburi mai nisan kilomita 150 a Arewa da birnin Bangkok.

Ɗimbin birrai sun keto a guje suka riqa faɗa da juna suna warwason abincin da aka shirya masu, yayin da maziyarta da mutanen yankin ke cigaba da tururuwar zuwa wajen.

An kai nau’o’in abincin da aka tsara zuwa wajen wani bautar gargajiya ne kafin birran su afka musu, waɗanda galibi kayan marmari da aka ajiye su kashi-kashi.

Yayin da birran ke ci gaba da dabdala, sai masu shirya bikin suka nuna bikin fa ba na birrai kaɗai ba ne, suka shiga aka riƙa damawa da su.

“Wannan dabdala ta birrai ta samu nasara, kuma hakan yana ƙara taimakawa wajen bunƙasa harkar yawon buɗe-ido a Lopburi a tsakanin ƙasashen duniya duk shekara,” inji Yongyuth
Kitwatanusont, wanda ya ƙirƙiro bikin.

Ya ce, “A baya akwai kimanin birrai 300 a Lopburi kafin su ƙaru zuwa kusan 4,000 daga baya.

“An san Lopburi da sunan birnin birrai, wanda ke nufin mutane da birrai suna iya rayuwa cikin jin daɗi da lumana.”

Za a iya ganin haka ta yadda wasu birran suke hawa kan maziyarta ba tare da tsoro ba, haka sukan hau kan motoci da tebura.

A wasu lokuta birran sukan bar ɗimibin abincin da aka tanada masu su riqa yin wasu abubuwan da suke sha’awa.

“Akwai wani biri da ya hau gadon bayana, a daidai lokacin da nake shirin ɗaukar hoton kaina da waya. Ya wafci tabarau din da ke idona ya ruga ya hau turken wutar kan hanya yana kokarin ya cinye shi,” inji Ayisha Bhatt, wata malamar Ingilishi ’yar Kalifoniya da take aiki a Thailand.

Sai dai masu kallo sukan yi taka-tsantsan kada birran su sace masu kaya.

“Mukan kula da su, maimakon barin su ga birran. Rashin yin nesa da su ya fi,” inji Carlos Rodway, wani ɗan yawon buɗe-ido daga garin Cadiz na ƙasar Spain, wanda ya ce a baya wani biri ya ɗauke masa wani abu ya haye sama.

Bikin na bana mai taken “Birrai na ciyar da birrai” ana shirya shi ne a Lopburi fadar yankin don nuna jin daɗi kan yadda birrai suke jawo masu yawon buɗe-ido.

By Editor