Jarumai ake tura wa mota a Kannywood, inji Furodusa Yakubu Baba

“Ni ne furodusa na farko a ƙananan yaran Kannywood”

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

A yau shafin Nishaɗi na Blueprint Manhaja ya gayyato wa masu bibiyar mu ɗaya daga cikin matasan da suka yi sammako a masana’atar Kannywood, matashin da ya tsunduma harkar fim tun ana yi masa kallon shekarunsa ba su kai ba, wanda hakan ya ba shi damar zama furodusa na farko a Kannywood mafi ƙananan shekaru, inji shi. Idan kun shirya, ku biyo mu, ku ji tattaunawar Manhaja da Yakubu Bala Baba tare da Wakilinmu IBRAHIM HAMISU:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu?

YAKUBU: Sunana Yakubu Bala Baba. Mai shirya finafinai, kuma darakta a masana’atar Kannywood. Kuma za ka iya cewa, komai da ruwanka a masana’antar Kannywood, domin har ‘Acting’ Ina yi.

Ko za ka ba mu taƙaitaccen tarihinki?

An haifeni a Gwammaja Kano, na yi karatun firamare  a Dala Primary, na yi karatun sakandare a GSS Dala, wato Gwammaja one, sanna  na yi makarantar Legal, inda na karanci Law. Ni ne ‘producer’ na farko a Kannywood a cikin ƙananan yara, don haka tun Ina shekara 25 na fara fim nawa na kaina.

Ta yaya aka samu kai a masana’atar fim ta Kannywood?

Na tashi Ina kallon Indiya tun Ina yaro saboda tsabar son Indiya idan ka shiga ɗakin mamana za kaga duk na liqe su da hotan jaruman Indiya, madhurri, Surfebi, Amita da sauran su. Na fara rubuce-rubuce, sanann na fara zuwa ƙungiyoyi ana korata, saboda na yi yaro lokacin, domin ban kai munzalin shari’a ba.

Sai muka zama abokai da wani jarumi Gagare, wato Ahmed Sani, Jarumin Sarauniya, lokacin shi ne baban jarumi kuma sai ya zama muna yawan zama ana abota koda yaushe,  sai na faɗa a gida Ina son fitowa fim, Ina son na fara fitowa a finafinan Hausa, sai ta ce, anya ban yi ƙanƙanta ba, na ce, don Allah a bar ni  na yi nawa na kaina, wato ‘ex producer’, ai kuwa ta ce, idan za ayi min kamar nawa ne zai min, na ce, zan tambaya, na je na tambayi abokaina ‘yan wata qungiya dake Gwammaja, wato Dabo, sai aka ce ai sai ka kashe dubu ɗari za kai fim.

Lokacin dubu ɗari kamar miliyan biyu ta ke, dan ta fi miliyan ɗaya. Aikuwa na je na gaya mata lokacin na saida wani gidana anan Tudun Bojuwa dubu ɗari biyu da hamsin, sai na ware dubu ɗari sai ƙungiyarsu kabiru Nakwango da Malam Inuwa na ce ga shi su yi min Fim. Take suka rakoni suka ce na yi ƙanƙanta sun ganni da uban kuɗi, masu yawa kuma na yi ƙanƙanta da shekaruna. Da aka zo gida tambaya, sai mahaifiyata ta ce, “Ina san Yakubu, saboda yana faranta min, duk abinda na ce ya yi, yana yi, don haka bana san ni ma na qi cika masa burinsa matuƙar bai saɓa waa shari’a ba.”

Farkon zuwanka masana’antar Kannywood da me ka fara?

Da fim nawa na kaina na shiga harkar, banyi yaron kowa ba ban yi yawan seling ba, da daraja ta na zo fim sai da na yi shekara 25 na yi uban gida ɗaya tamkar da dubu, wato Producer Hayatudden da ake cewa, Baba Hayatu. Mutum na gari mai dattako mai nutsuwa da tsoron Allah, mai gudun duniya da abinda ke cikin ta, kullum burinsa yaya zan yi abinda zai zama abin yabo ba abin banza ba, ba abin Allah wadai ba. Shi ne wanda ya yi min fim da na rokeshi na ce Ina so na fara fim a matsayin jarumi, sai ya ce, Yakubu ka nemo labari ko ka nemo jarumai masoyanka waɗanda ba za su baka matsala ba ka yi cast, zan kashe maka ko nawa ne ka zama jarumi da iznin Allah ba jarumin Kannywwod ba ko ana ɗauko aiki daga Amurka ne insha Allah zan ɗauko maka shi,  a nan mu ka yi aikin aka gama ya kashe mini kusan miliyan uku fim mai suna ‘Akasi’ na company Alhayat films Production ya fito, ni kuma a matsayin jarumi.

Da yawan mutane an fi sanin ka da ‘Producer’, wato Mai shiryawa. Me ya sa ka fi son cangaren shiryawa?

A’a, ba wai na fi son  ‘producer’ ba, da shi a ka sanni, shi na fara kamar yadda na gaya maka, amma sai zamani ya zo producer a banza darakta abanza, kowanne ma’aikaci a banza, jarumi ya fi kowa suna, ya fi kowa daraja, sai muka tuna ashe mota muke turawa ta tashi ta bule mu da ƙura, sai kowanne darakta ya ce, ya zama jarumi, kowanne producer ya dawo ‘acting’ gidan gwamna jarumi ake nema gidan shugaban ƙasa jarumi ake nema, tallan company jarumi ake nema komai jarumi.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa ka shirya?

Za su kai 30 nawa na kai na, kamar ; ‘Yan kwalta’, ‘Sarauniyar Kyau’, ‘Tabare’, ‘Dukiyar marayu’ da sauran su. Amma na mutane suna nan da yawa yanzu haka zan yi wani katafaran fim mai suna ‘Hamshaƙan Mata’ wanda zan zuba mata 60 a ciki maza barkatai, zan kashe kuɗi sama da miliyan biyar nawa ne na kaina yanzu haka labarin ake rubutawa siyasar ce ta sa na ɗan ja baya saboda jaruman nawa sun ta fi siyasa, amma ba da daɗewa ba za mu fara, insha Allah.

Daga lokacin da ka fara zuwa yanzu waɗanne nasarori za ka iya cewa ka samu a harkar ?

Wallahi bazan iya faɗin adadin su ba, sai dai na ɗan faɗi wasu, na mallaki gida da sana’ar fim, na sai filaye, na samu jari, na samu manyan mutane, ‘awards’ da na samu ya fi 20, karamci kala-kala na samu babu abinda za a cewa wa Allah sai godiya.

Wane irin  ƙalubale ka ke fuskanta a masana’atar Kannywood da ga fara wa zuwa yanzu?

kowanne abu kwai farin ciki akwai kishiyarsa, na sha ƙalubale kala-kala, musamman wanda ka taimaka wa shi ke son ya kai ka ƙasa a wannan masa’antar tamu haka abin yake masu kirkin ‘yan halak ɗin ba su da yawa.

Da wa ka ke koyi a masana’atar Kannywood ?

Ababan koyi na mutanen suna da yawa gaskiya, yayyyena ne da iyayen gidana. Na farko Baba Hayatudden, wato Haba hayatu, ya kasance uba a guna; yayana, wanda ya yi min abin halaccin da bazan taɓa mancewa ba, ta hanyar nusar da ni kura-kuraina, idan na yi ba daidai ba zai kira ya yi min faɗa. Masoyi na haƙiƙa, yana wuya na yi kuskure kamin faɗa.

Tabbas masoyi ne. Ɗaya ogana da ya zama zakaran gwajin dafi shi ne, Muhammad Salisu na Tauraruwa TV, ya kasance mutum ne mai daraja da karamci nagari mai bani shawarwarin cigaban rayuwa, mai qaunar cigabana komai nawa. Yanzu haka za mu fara ɗaukar shiri mai dogon zango a cikin mutane sama da dubu ya ɗauko ni, ya ce, ni ne zan yi masa producer na babban gidan tv wanda kowa yasan tauraruwa wannan abin alfahari ne a gare ni, abin tarihi ne a gare ni. Ina masa fatan alhare shida zuri’arsa, ubangiji y Ya kula da su bakiɗaya da abokin aikinsa Abdurrahaman manaja Allan Ya biya musu buqatu na alheri duniya da lahira. Allah Ya ɗaukaka wannan gidan tv namu. Waɗannan su ne allon kwaikwayona bakiɗaya Kannywood, ina san nazama mutum mai taimakon na ƙasa dani kamar yadda suka taimakeni, Ina san na zama mutum mai jin-ƙan marar ƙarfi kamar yadda saka jin-ƙaina da ƙaramin kamfanina duk da tsoho ne sama da shekara 20 suke ƙoƙarin ya ɗago babu abinda zance wa mutanen nan ukun saidai Allah ya ba su gidan aljanna. Na gode ƙwarai.

Wane tsari ka ke ganin za a iya yi wajen kwararowar mutane cikin Kannywood musamman mata?

Mata suna da matsala; suna da haɗari gaskiya, kada su shiga saida yardar iyayensu, saboda muna da kwamiti mai ƙarfi ba a ɗaukar macen kan titi sai da izinin iyayenta, saboda wasu matan aure ne suna zuwa su shiga kai tsaye sai angama ai ta faɗa da mazaje da iyaye, karshe mutum ya yi asara, ni kamfanin gwammaja na kori mata sama da 80 masu buƙatar shiga Ina korarsu wasu basa cika sharaɗi, wasu ba fim ba ne zai kawosu kawai suna buƙatar su yi suna dan su bunƙasa karuwancinsu; manyan mutane su san su, su ƙara farashin, don haka suna jin dokokina sai suka gudu, ba su ƙara dawowa ba.

Ko za ka iya tuna wani fim da ka sha wahala yayin gudanar da shi?

Wani fim ne mai suna Ibro Rabon Wahala’ na fi shan wahalarsa, sunan fim ɗin shi ya bini mutanan farko ma na sha wuya ‘Akasi’  shima na sha wuya wanda ni ne jarumi, kuma ni ne ‘producer’ subhanallah! Gaskiya na sha wuya da ƙalubale iri-iri.

Menene burinka a masana’atar fim ta Kannywood?

Burina bai wuce mu ji tsoron Allah ba, kada mu yi fim sai mai ma’ana, ka da mu yi na fasadi da fasiqanci, wanda idan mun koma ga Allah za a tambaye mu a kansa, mu tsare al’aurarmu mu tsare mutuncinmu, komai mu yi don Allah, shine zai bada lada akan komai kuma nasara tana samuwa, domin masoyana tako ina suna ɓulɓulowa gari gari, ƙasa-ƙasa, sai godiya ga Allah. Kamfanin Gwammaja Entertainment Kano muna gode wa Allah.

Muna godiya da lokacinka.

Ni ma na gode.