Wani alƙali a ƙasar Zimbabwe da ’yan sanda suka bayyana cewa suna neman sa saboda kisan gilla da aka yi wa matarsa ya kashe kansa a wata coci.
Alƙalin da ya kashe kansa, Evans Zinzombe, mai shekaru 36, ya kasance yana vuya ne daga ’yan sanda bayan da ya kashe matarsa, Pholomina Mabika, mai shekaru 32, a ranar Laraba, 7 ga watan Disamba.
An ruwaito cewa, ya shaƙe Pholomina har lahira da hannunsa, sannan ya cigaba da yi wa gawarta fyaɗe a gaban ’ya’yansu; ‘yar shekara 12 da kuma ɗan shekara 7.
Mai magana da yawun ’yan sandan, mataimakin kwamishina Paul Nyathi wanda ya bayyana alƙalin da ake nema ruwa a jallo ya ce, “Rundunar ’yan sandan jamhuriyar Zimbabwe na neman bayanan da ka iya kai ga kama Alƙali Evans Zinzombe (36), wanda ake nemansa da laifin kisan kai wanda ya faru a ranar 07 ga Disamba 2022 a wani gida a Cowdray Park a Bulawayo.
“Wanda ake zargin ya kutsa cikin ɗakin da matarsa Pholomina Mabika ’yar shekara 32, ’yarsa, 12 da kuma ɗansa, 7 inda ya shaƙe ta har lahira.
“An rahoto cewa wanda ake zargin da matarsa na fama da rikicin aure wanda ya tilasta musu kwanciya a ɗakuna daban-daban.
“Bayan kisan gillar da aka yi, wanda ake zargin ya cigaba da lalata da gawar a idon ’ya’yansa. Yaran sun kwana tare da gawar kafin a kai rahoton ’yan sanda da safe.
“Rundunar ’yan sandan jamhuriyar Zimbabwe ta gargaɗi jama’a game da yin tashin hankali wajen warware rikicin cikin gida.
“Rundunar ’yan sanda za ta tabbatar da cewa doka ta ɗauki matakinta kan waɗanda ake zargi da aikata muggan laifuka kamar kisan kai da fashi da makami.
Daga nan ne aka gano gawar Alƙali Evans Zinzombe a rataye a rufin wani coci a unguwar Cowdray Park na Bulawayo.
Da ta ke tabbatar da mutuwarsa, rundunar ’yan sandan ta ce, a cikin wata sanarwa da ta fitar, “An tsinci gawarsa rataye ne a jikin rufin ƙarfe a wani coci da ke Cowdray Park.”
’Yan sandan sun ɗauki mutuwarsa a matsayin kashe kai.
