Allah Ya yi wa Batulu Alhassan Baba Ahmad Dantata rasuwa tana da shekara 40.
Marigayiyar ɗaya ce daga cikin jikokin hamshaƙin ɗan kasuwar nan na Kano, Alhaji Aminu Dantata.
Majiya daga ahalin ta ce, Batulu ta rasu ne a Kano bayan fama da rashin lafiya.
Marigayiyar ta rasu ta bar mahaifiya, Hajiya Ummul Khair Aminu Dantata, wadda ta kasance ‘yar fari Alhaji Aminu Dantata, sai kuma mahaifinta, Alhaji Baba Alhassan Ahmad Dantata.
Ana sa ran za a yi mata Jana’iza da misalin ƙarfe 10 na safe a babban masallacin Koki da ke Kano a wannan Talatar.
