Taron Afirika KILAF Award 2023: shirye-shirye sun kankama

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A daidai lokacin da a ke ci gaba da shirye shiryen bikin Bajekolin finafinai na Afirka ‘African Indigenous Language Filims’. Mai taken ‘Kano Indigenous Languages Of Africa Film Market & Festival’ KILAF AWARD, da aka saba shiryawa duk shekara a garin Kano. A yanzu haka dai an kai ga matakin tantance finafinan da suka shiga gasar domin fitar da waɗanda za su kai matakin matakin cancanta da kuma wadanda ba su kai ba.

Alƙalan gasar dai su bakwai ne da suka haɗa da Victor Okhoir, Emmanuel Emascalu, Charlas Okwuowulu, Falakemi Ogungbe, Izu Ojukwu, Charity Torut, da Alwine Allen.

A wannan shekarar dai an samu ƙarin finafinai da suka shiga gasar fiye da shekarun da suka gabata, inda aka samu finafinai guda 46 suka shiga daga ƙasashen duniya daban-daban da su ka haɗa da Najeriya, Masar, Afirka ta Kudu, Tunusiya, Ghana, Tanzaniya, Aljeriya, Ajantina, Benin, Botswana, Kamaru, Kodebuwa, Jamus Gini Bissau, Kenya, Malawi, Mozanbiq, Potugal, Amurka da kuma Zumbabuwe.

Kamar yadda daraktan gudanarwa ga bikin KILAF AWARD 2023 Nasir B. Muhammad ya yi mana qarin bayani dangane da taron na bana, ya ce

“A wannan shekarar an samu sauye sauye, saboda ci gaban zamani da a ke samu, don haka tantancewar ma ta onlayin ake gudanar da ita, saboda alƙalan sun fito ne daga sassa daban-daban na duniya don haka sai aka tsara gudanar da tantance su ta onlayin, amma a mataki na ƙarshe za a haɗu a waje guda don fita da sakamakon gasar.”

Dangane da shi taron kuwa cewa ya yi, “to kamar yadda muka saba a baya, a wannan ma dai akwai babban taro da muke yi a BUK wanda za a karanta maƙaloli. Wannan taron yana da muhimmanci a cikin tsarin shirye shiryen mu. Sannan akwai babban aji na koyar da harkar fim wanda shi ma na bana ya zo da wani tsari na dabam domin mun samar da qwararrun masana a kan harkar fim da za su koyar. To ka ga duk wanda yake jin kansa shi mai sana’ar fim ne, kamata ya yi ya zo ba sai an gayyace shi ba.

Sannan akwai abincin Afirka da ake gudanarwa a taron, don haka muna gayyatar duk wanda yake ganin ya ƙware a fagen tsara abinci na Afirka. Sannan akwai finafinai da za a nuna su a sinima kuma waɗanda suka shirya finafinan za a gan su a wajen da duk wanda yake da wata tambaya ya yi musu, saboda haka ni ina ganin wannan wani abu ne kamar an haɗa ƙarfi da qarfe, domin a ga mun kai wani gaci.

Sannan kuma akwai cin abinci na musamman da za a shirya wa baƙi sai kuma ranar award da za a gayyato baqi daga ko’ina domin su halarci wajen, don haka nake ganin duk wani mutum da yake da kishin ci gaban harkar fim, taron na sa ne ba sai an gayyace shi ba, don shi ma mai gayyata ne, domin dama ce da zai haɗu da mutane kuma ya koyi abubuwa masu damar gaske, kuma dandali ne na shirya mu’amala da kuma kasuwanci tsakanin mu da abokan harkar mu na ƙasashen Afirka. Don haka muna fatan za a ba mu haɗin kan da ya kamata.”

By Editor