Ƙarar bindiga ta tarwatsa ‘yan Majalisar Ribas

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

‘Yan Majalisar Jihar Ribas sun yi rububin neman mafaka don tsirar da ransu bayan da suka ji ƙarar bindiga a wajen majalisar alhali suna tsaka da zama a wannan Litinin.

Sabon rikici ya ɓarke a Majalisar Dokokin Jihar Ribas biyo bayan jita-jitar da ake yaɗawa cewa majalisar ta fara shirin tsige Gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara, musamman ganin yadda majalisar ta tsige shugabanta kuma ɗan-ga-ni-kashenin gwamnan, wato Edison Ehie.

MANHAJA ta tattaro cewar, Gwamna Fubara a ya yi dirar mikiya da a majalisar da safiyar Litinin inda aka ji harbin bindiga da barkonon-tsohuwa a wajen majalisar, lamarin da ya sa ‘yan majalisar kowa ya tsere don neman mafaka.

Haka nan, ya zuwa haɗa wannan labari, an ga wasu masu zanga-zanga a harabar majalisar.

Wannan na zuwa ne bayan da aka samu aukuwar gobara a ginin majalisar a ranar Lahadin da ta gabata.

Duk da dai babu wani cikakken bayani kan dalilin aukuwar gobarar, amma wata majiya ta ce rashin jituwar da ke tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamnan jihar kuma Ministan Abuja a yanzu, ya jima yana gwara kan ‘yan majalisar.

Da yake bayani sa’ilin da ya ziyarci Majalisar, Gwamna Fubara ya ce babu wani laifi da ya aikata da ya cancanci tsigewa daga majalisar jihar.

“Me zai hana su fito su faɗa wa al’ummar Ribas laifin da na aikata da zai sa a tsige ni,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Ina mai tabbatar wa al’ummar Ribas zan ci gaba da tabbatar da kuna samun ribar dimokuraɗiyya. Kuma zan yi magana da ‘yan harida a lokacin da ya dace.”

By Editor