Mace Manjo-Janar ta farko a Sojin Nijeriya ta kwanta dama

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Mace ta farko da ta kai matsayin Manjo-Janar a sojin Nijeriya, Aderonke Kale, ta riga mu gidan gaskiya

Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana marigayiyar a matsayin tauraruwa wadda ta nuna ƙwazo da cikakkiyar biyayya a bakin aiki a halin ratuwarta.

Rundunar ta ce, ƙwazon da marigayiyar ta nuna a bakin aiki a halin rayuwarta ya bai wa jami’ai da dama samun cigaba a bakin aiki.

Cikin sanarwar da ya fitar, Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Brigadier General Onyema Nwachukwu ya ce, “Rundunar Sojin Nijeriya ta samu labarin rasuwar Manjo Janar Aderonke Kale (mai murabus) CFR mni, a ranar Laraba, 8 ga Nuwamban 2023.”

Rundunar ta ce marigayiyar ta bada gudunma mara misaltuwa ga cigaban rundunar a halin rayuwarta.

By Editor