Daga MUHAMMAD SULAIMAN ABDULLAHI
Sau da yawa ina mamakin irin halin da yara suka shiga a wannan zamani namu (ba yara kadai ba, ina magana ne a yanzu a kan yaran). Da, yaro a gidansu kamar wani sarki yake, komai a yi masa, ana ji da shi ana haba-haba da shi, ana kula da shi, ana yi masa dukkanin wani abin da ya kamata, har ma da wanda bai kamata ba a wasu lokuta, amma a yau, da yawa daga cikin yara, sun shiga halin ni-‘yasu!
Daga cikin abubuwan da nake iya tunowa a rayuwar yarinta, shi ne irin yadda yara a da suke fagamniya a cikin shagulgula iri-iri na morewa da lolewa da cashewa a rayuwar duniya, su tsoma biyar, su yi bushashar su yadda suke so. Ina tuno ko da a harkar abinci, a da, yaro sai an nemo shi ya ci abinci, wani lokaci har da duka, da zagi, da fada, kafin yaro ya ci zo gida ya ci abinci.
Haka nan, tuna lokacin shayi. Idan aka yi wa yaro shayi, sai ka ga ya koma wani dan karamin attajiri. Masu kawo kaji na yi, masu zabi na yi, masu yadudduka da kaya iri-iri. Ga kifi ga nama da farfesu baja-baja, amma a yau wani yaron ko cikakkiyar fara ba ya samu idan an yi masa shayi.
In na tuna da wutar lantarki a da, sai in ga kamar da wahala a iya dowowa kamar da. Wuta da, baya-bayan nan, sai a dade ba a dauke ba. Har wani fim din qarshe ake kallo, ba na mantawa ranar Asabar da daddare, Lahadi da safe kuma a kalli Indiya, kuma duk da wutar lantarkin gwamnati, amma a yau, yara sun fi kowa sanin janareto, a inda ma ake da jannareton kenan. Wasu ba su ma san wani abu wai shi NTA da CTV ba.
Tuna lokacin shagulgulan sallah! Alewoyi da su Suwi Kampo, da barka da sallah, da Toffee da Nasco biskit, wasu duk na dade da daina jin labarinsu.
A gaskiya rayuwar yara tana cikin wani hali. Ya kamata manyan da suke aiki tuquru wajen kuntata rayuwar yara su sake tunani. Manyan nan, ku sani cewa idan kuka yi rahama ga na kasa da ku, sai Allah ya yi muku rahama ku ma.
Yara suna daga cikin wadanda Allah yake karvar addu’arsu da wur-wuri, saboda ba su zubarwa da kowa komai ba, yawancin yara, duk da suna da kiriniya, amma a zamanin da, suna da gaskiya, ba yanzu ba da wasu yaran suka zama kamar manya ta fuskar iya zalunci da almundahana, duk a sakamakon munanan halayen manya.
Abubuwan fada game da yara a jiya da yau, suna da yawa, amma dai, nan kadan ne, kai me za ka/ki iya tunowa a zamanin yarinta?
Abdullahi, mai sharhi ne kan lamuran yau da kullum, ya rubuto daga Beijing ta Chana.
