Gwamna Fintiri ya yi nasara a Kotun Ƙoli

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ƙoli mai zamanta a Abuja, ta tabbatar da Ahmadu Fintiri a matsayin zababben Gwamnan Jihar of Adamawa.

Cikin hukuncin da ya karanto tayin zaman Kotun a ranar Laraba, John Okoro, ya yi watsi da karar da ‘yar takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Aisha Dahiru, ta daukaka a kan Fintiri saboda rashin cancanta.

Kotun ta ce halin da Kwamishinan Zaben jihar, Hudu Ari, ya nuna hali me na rashin kan gado laifi babba.

Mai Shari’a Okoro ya kara da cewa, baturen zabe ne kadai doka rmta bai wa ikon sanar da sakamakon zabe domin kauce wa kowane irin hayaniya.