Tsaro: Gwamnatin Kano ta yi alƙawarin taimaka wa Gwamnatin Tarayya kan yaƙi da ta’addanci da satar mutane

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin mara wa shirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya na daƙile illolin rashin tsaro da ke dagula zaman lafiya a kasar nan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan alƙawarin ne a ranar Juma’a a lokacin da ya karɓi baƙuncin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Alhaji Muhammad Idris a ziyarar ban girma da ya kai gidan gwamnati.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya ce ya dace a hada kai da gwamnatin tsakiya domin daƙile wuce gona da iri domin dawo da ci gaban ƙasa.

Alhaji Yusuf ya yabawa Shugaba Tinubu bisa yadda ya yi biyayya ga kiran da ya yi na sake bude iyakokin Nijeriya da wasu ƙasashe, matakin da zai taimaka wajen rage wahalhalun tattalin arzikin ƙasar.

Ya kuma bayyana ziyarar a matsayin wacce ta dace la’akari da yadda ta ke gudanar da harkokinta da masu ruwa da tsaki ciki har da ‘yan kasuwa da suka yi alƙawarin yin duk abin da ya kamata na marawa gwamnatin tarayya baya a ƙoƙarin da take yi na inganta ƙasar nan.

Tun da farko, Ministan, Alhaji Muhammad Idris Malagi ya ce shi ne ya jagoranci tawagar manema labarai na fadar shugaban ƙasa zuwa Kano, kuma ya gana da ‘yan Nijeriya daga sassa daban-daban, inda ya bayyana irin abubuwan da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi domin kyautata rayuwa ga ‘yan Nijeriya.

A cewar Ministan, “Mun zo ne domin neman haƙuri da fahimtar juna a lokacin wasu ƙalubalen tattalin arziki da muke fama da su. Hakika wasu ƙalubalen na buƙatar dukkan ‘yan Nijeriya su jure domin mu samu ci gaba a wajenmu baki ɗaya.” ministan

Ya kuma bayyana fatansa na cewa, wannan ikirari na Gwamna Yusuf da Kotun Ƙoli ta yi zai kara wa gwamnan kwarin gwuiwa wajen ƙara zage damtse wajen ganin an samar da ribar dimokuraɗiyya ga al’ummar Kano.

Ministan ya ci gaba da cewa, haɗakarsa da ‘yan kasuwa za ta samar da sakamako mai kyau bisa la’akari da yadda Kano ta kasance cibiyar kasuwanci ba kawai a yankin Arewa ba har ma da faɗin ƙasar baki ɗaya.

Daga baya ya mika takardar shaidar tutar ƙasa ga gwamnan tare da ba da shawarar a sayo tutoci masu yawa don amfani da su a gine-ginen gwamnati da sauran ayyukan hukuma a jihar.

By Editor